Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 17:42:16    
Yanayi da zaman fararren hula na jihar Guangxi sun samu kyautatuwa sosai sakamakon yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki

cri

Gundumar Gongcheng ta 'yan kabilar Yao mai cin gashin kai tana kudu maso gabashin birnin Guilin na jihar Guangxi. Yawan mutanen gundumar bai kai dubu 300 ba, kuma rabi da ke cikinsu 'yan kabilar Yao ne. Ana iya ganin wuraren samar da iskar gas da aka samu daga taki a kusan ko wane gida na kauye. A wani kauye na kabilar Yao da yawan mutanensa ya kai 200 kawai, wakilinmu ya gano cewa, akwai wurare 56 da ake iya samun iskar gas da aka samu daga taki, kuma yawan gidajen kauyen da ke yin amfani da iskar gas ya kai kashi 96 cikin dari.

Rong Wenxi, wani manomi na kauyen ya bayyana cewa, yanzu suna yin amfani da iskar gas wajen yin girki da kuna fitila, ba kawai sabo da iskar tana da tsabta sosai ba, har ma sabo da farashin iskar yana da araha. Ya ce, " Iskar gas da ake samu daga taki tana da araha a gwargwado. Idan muka yi amfani da iskar gas, to za mu kashe a kalla yuan 92 a ko wane wata, amma idan muka yi amfani da iskar gas da aka samu daga taki, yuan 32 ya isa."

1  2  3