Malam Lin Kang, mataimakin babban manajan kamfanin yawon shakatawar kasa da kasa ta Sin mai kula da harkokin yawon shakatawa a kasashen waje ya bayyana cewa, yanzu, manyan kamfanonin yawon shakatawa na kasar Sin daban daban suna sa ran alheri ga makomar kasuwannin yawon shakatawa na Afrika. Ya ce, "daga cikin kasashen Afrika wadanda Sinawa ke samun damar zuwa yawon shakatawa, akwai Masar mai dogon tarihi, inda dala da haikalai da sauran wurare masu ni'ima wadanda suka shahara sosai a duniya suke. Ban da wadannan kuma masu yawon shakatawa suna sha'awar wurare masu ni'ima na kasar Kenya da kasar Afrika ta Kudu ainun. Afrika wata nahiya ce mai al'ajabi. Ina kyautata zaton cewa, nan da shekaru uku ko biyar masu zuwa, yawan masu yawon shakatawa na kasar Sin wadanda za su yi yawon shakatawa a nahiyar Afrika zai dauki rubu'in jimlarsu da ke yawon shakatawa a kasashen waje."
Wani jami'in hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, nan gaba, kasar Sin za ta sa kaimi ga jama'ar Sin da su yi yawon shakatawa a kasashen Afrika, kuma za ta ci gaba da yin kokari wajen kara mayar da kasashen Afrika bisa matsayin kasashe da jama'ar Sin ke iya zuwa yawon shakatawa.
Jama'ar Sin suna kara fahimtar nahiyar Afrika ta hanyar yin yawon shakatawa a Afrika. Bayan da masu yawon shakatawa na kasar suka komo nan kasar, su kan tuna da Afrika. Malam Luo Hong ya ce, ya ji matukar farin ciki da zaman rayuwa tare da aminansa na Afrika. A duk lokacin da ya kallaci hotuna da ya dauka a Afrika, sai ya kan yi fatan alheri ga nahiyar Afrika mai kayatarwa, kuma ya roki Allah da ya kiyaye duk jama'ar kasashen Afrika da abubuwa masu rai da ke zama a nahiyar nan. (Halilu) 1 2
|