Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 17:05:11    
Afrika ta zama sabuwar nahiya da Sinawa ke sha'awar zuwa yawon shakatawa

cri

Dala mai al'ajabi na kasar Masar da kololuwar dutse mai suna Kilimanjaro na kasar Kenya wadda ita ce kololuwa mafi tsayi a Afrika, da mahakan zinariya da masana'antun lu'ulu'u na kasar Afrika ta Kudu, dukanninsu wurare ne da Sinawa ke sha'awar zuwa yawon shakatawa. A shekarar bara, yawan Sinawa da suka yi yawon shakatawa a nahiyar Afrika ya kai dubu 110, lalle, yanzu, Afrika ta zama sabuwar nahiya da Sinawa ke sha'awar zuwa yawon shakatawa.

Malam Luo Hong, mai gida ne na wani shahararren kantin sayar da kyat a kasar Sin. Ya taba kai ziyara a nahiyar Afrika har sau 10. Da ya tabo magana a kan ziyarar da ya yi a "Tafkin Nakuru" na kasar Kenya, sai ya jiku da cewa, "yau da shekaru shida da suka wuce, karo na farko ke nan da na kai ziyara a nahiyar Afrika, da na ga jajayen tsuntsaye masu dimbin yawa da ake kira "Falamingo" a Turance a kan "Tafkin Nakuru", sai na fara kaunar Afrika ainun."

Yanzu, Sinawa da ke zuwa yawon shakatawa a nahiyar Afrika, daidai kamar yadda Malam Luo Hong ke yi, kullum sai kara karuwa suke yi. Yawan kasashen Afrika wadanda Sinawa ke iya zuwa yawon shakatawa bisa aljihunsu, ya kai 17.

Dalibi Guo Jia wanda ke karatu a Jami'ar Jama'ar Sin ya taba yin yawon shakatawa a kasar Afrika ta Kudu yau da shekaru biyu da suka shige. Da ya tabo magana a kan Afrika, sai ya nuna yabo cewa, "na yi yawon shakatawa ne a kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2004, kasar nan kasa ce mai ni'ima kwarai. Ga kungurmin daji da manyan filayen ciyayi da sauransu wadanda nake sha'awarsu ainun. A lokacin da muka tafiye a wadannan waurare cikin motar jif, sai mun ga jakunan dawa wadanda ke ketare hanyar, wannan ya burge ni kwarai. "

1  2