Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-27 19:16:42    
Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi alkawarin yin hidima da kyau ga kafofin watsa labarai na kasashen duniya

cri

Kazalika, Mr. Liu Qi ya fayyace, cewa yanzu sassan da abun ya shafa na gwamnatin kasar Sin ta rigaya ta tsara wassu dokoki kan batun daukar labarai da 'yan jarida na kasashe daban daban za su yi lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Za a kaddamar da wadannan dokoki da kuma aiwatar da su ne a shekara mai zuwa bayan da aka amince da su bisa ajandar shari'a. Ban da wadannan kuma, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing za ta buga wani ' Littafin ba da jagoranci ga 'yan jarida baki a taron wasannin Olympic na Beijing'.

Yanzu, sassan da abun ya shafa na gwamnatin kasar Sin tana kwaskwarimar dokokin shari'a da abun ya shafa domin tsara manufofin musamman da kuma daukar matakin saukaka aikin duddubawa daga gwamnatin kasar, ta yadda za a samar da kyakkyawan sharadin aiki ga 'yan jarida na ketare lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Dadin dadawa, Mr. Liu Qi ya yi nuni da, cewa lokacin da ake yin hidima da kyau ga 'yan jarida wadanda suka yi rajista, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai kuma yi shirin kafa wata cibiyar 'yan jarida da ba su yi rajista ba domin yin hidima da kyau ga 'yan jarida da yawansu ya zarce dubu goma, ta yadda aminai na kafofin watsa labarai za su samu sauki wajen daukar labaru da kuma jin dadin zama da aiki a Beijing.

Mr. Kevin Gosper, shugaban kwamitin watsa labarai na kwamitin wasannin motsa jiki na duniya shi ma ya yi jawa a gun taron, inda ya hakkake, cewa labuddah kwamitin shirya taron wasannin Beijing zai iya cika alkawarinsa na yin hidima da kyau ga kafofin watsa labarai na kasashe daban daban wajen daukar labarai game da taron wasannin Olympic na Beijing. Ya kuma ce, Sinawa masu sauraron ra'ayoyi ne mafiya kyau a duniya. ( Sani Wang )


1  2