Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-27 19:16:42    
Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi alkawarin yin hidima da kyau ga kafofin watsa labarai na kasashen duniya

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, a nan birnin Beijing, aka yi babban taro na farko na kafofin watsa labarai na kasa da kasa na taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing. A duk tsawon lokacin babban taron, shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Mr. Liu Qi ya yi alkawari da gaske, cewa kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijig zai yi hidima da kyau ga kafofin watsa labarai na wurare daban daban na duniya a lokacin da ake gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Babban taron da aka yi a wannan gami, wani taro ne kan ayyukan hidima da za a yi ga kafofin watsa labarai na taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing. A gun taron da aka shafe kwanaki biyu ana yinsa, wakilai fiye da 300 daga kamfanonin dillancin labarun da jaridu da kuma mujalloli na wurare daban daban na duniya, wakilan kwamitin watsa labarai na kwamitin wasannin Olympic na duniya da kuma sassan da abun ya shafa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun yi nazari da musaayar ra'ayoyi sosai game da batun bayar da labarai da kuma aikin hidima ga kafofin watsa labarai dangane da gasannin da za a yi a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Mr. Liu Qi, sakataren kwamitin birnin Beijing na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi jawabi a gun taron, inda ya furta, cewa ta wannan taro, za a iya kara yin tuntubar juna tsakanin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da dimbin aminai na kafofin watsa labaru, da gane bukatun ' yan jarida na kasashe daban daban, da sauraron ra'ayoyin jama'a ,da kuma kyautata ayyukan hidima domin aza harsashi mai inganci ga ayyukan hidima ga kafofin watsa labaru wadanda za su bayar da labarai game da wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Daga baya, Mr. Liu Qi ya jaddada, cewa yin hidima da kyau ga kafofin watsa labaru, wani muhimmin aiki ne na ayyukan share fage ga taron wasannin Olympic. ' Saboda haka', in ji shi, 'gwamnatin kasar Sin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing suke mai da hankali sosai a kai'. Sa'annan Mr. Liu Qi ya fadi, cewa al'ummar kaar Sin tana da kyakkyawar al'adar rikon amana. Kasar Sin, wata babbar kasa ce dake rikon amana, kuma gwamnatin kasar Sin gwamnati ce dake cika alhakin dake bisa wuyanta. Ko shakka babu gwamnatin kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi lokacin da take neman shirya taron wasannin Olympic, wato ke nan za ta samar da sauki da kuma yi hidima da kyau ga kafofin watsa labaru na kasashe da shiyyoyi daban daban na duniya wajen daukar labarai dangane da taron wasannin Olympic na Beijing.

1  2