Babban jigon bikin baje koli na kayayyaki masu aiki da lantarki da aka shirya a wannan shekara a kasar Sin shi ne "sauye-sauye a kayayyakin sadarwa a duniya". Da malam Lou Qinjian, mataikain ministan sadarwa na kasar Sin ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, "alal misali, wayar salula wadda mu kan yi amfani da ita wajen yin sadarwa, yanzu ta zama wani kaya ne na na'urar kwamfuta. Dalilin da ya haka shi ne, domin ana iya yin amfani da wayar salula kamar wayar tarho da telebijin da kayan shiga shafin tashar Internet. Sabo da haka yanzu ana fitar da kayayyaki masu aiki da lantarki ne domin yin amfani da su a fannoni daban daban."
Gaskiya ne, ko masana'antun yin kayayyaki masu aiki da lantarki da masaya dukanninsu sun sami ra'ayi daya sosai, wato wajibi ne, kayayyaki masu aiki da lantarki da ake fitarwa, ana iya amfani da su a fannoni daban daban.
Malam Yu Chong, mataimakin magajin gari na birnin Qingdao wanda ya shirya wannan bakin baje-koli na kayayyaki masu aiki da lantarki a kasar Sin a shekarar nan shi ma ya bayyana wa manema labaru cewa, "daga cikin dimbin kayayyaki masu aiki da lantarki iri na zamani da birnin Qingtao ya nuna a gun wannan bikin baje-koli, akwai wasu da za mu fitar da za su zama kayayyaki na sigar musamman na birninmu. Kayan nan na farko shi ne wayar salula, kayayyaki mabi mata su ne piyano mai aiki da lantarki da geta mai aiki da lantarki da kayayyakin DVD da makamantansu, sa'an nan sai kayayyakin motsa jiki masu aiki da wutar lantarki da wasan Internet da kuma kayayyakin motoci masu aiki da wutar lantarki. "
Birnin Qingdao wani birni ne mai kayatarwa da ke bakin teku na kasar Sin. A duk lokacin zafi, mutane masu dimbin yawa da ke fitowa daga wurare daban daban su kan yi runtuma zuwa birnin nan don yin yawon shakatawa. Hukumar birnin Qingdao ta bayyana cewa, tabbas ne, nan gaba za a kara gudanar da irin wannan bikin baje-koli da kyau a lokacin zafi, ta yadda wakilan kamfanonin yin kayayyaki masu aiki da wutar lantarki na duk duniya za su zo birnin Qingdao mai ni'ima don halartar bikin baje-kolin, su sami damar yawon shakatawa a birni da ya shahara a gida da waje. (Halilu) 1 2
|