Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-27 18:57:28    
Bikin baje-koli na kayayyaki masu aiki da lantarki da aka shirya a kasar Sin ke jawo hankulan jama'a sosai

cri

A kwanakin baya ba da dadewa ba, an shirya gagarumin bikin baje koli na kasa da kasa na kayayyaki masu aiki da lantarki na kasar Sin na shekarar 2006 a birnin Qingdao da ke bakin teku na gabashin kasar Sin. Masana'antun kera kayayyaki masu aiki da lantarki na kasa da kasa wadanda yawansu ya wuce 400, sun nuna sabbin kayayyakinsu iri na zamani a gun wannan bikin baje koli, don neman samun damar hadin guiwarsu.

Babban kamfani mai suna "Lenovo" na kasar Sin wanda ke shugabancin yin kayayyakin sadarwa na zamani a kasar, ya nuna sabbin kayayyakin sadarwa na zamani da ya fitar a gun bikin baje kolin. A gun bikin, Malam Du Jianhua, mataimakin babban direktan kamfanin ya bayyana wa menema labaru cewa, ana iya yin amfani da sabbin kayayyakin kamfaninsa wajen fitar da hotuna daga naura mai aiki da kwakwalwa zuwa akwatin telebijin don kallonsu, ta haka an kara samun ci gaba wajen yin amfani da kayayyakin nan biyu a fannoni daban daban.

A wannan shekara, karo na biyu ne , Malam Zhang Cida, wanda ke aiki a kamfanin yin kayayyakin masu aiki da lantarki da na sadarwa mai suna Mingji ya shugabanci kungiyar kamfaninsa wajen halartar bikin baje koli na kayayyaki masu aiki da lantarki. Ya ce, "yawan mutane da suke halartar wannan bikin baje koli na kayayyaki masu aiki da lantarki ya karu sosai, kayayyaki da aka nuna a gun wannan biki ma sun karu sosai. Amma a hakika dai, muna nuna kayayyakinmu ne musamman domin gwada wa masaya kyakkyawan samfurinsu. "

1  2