Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-24 17:13:57    
Ziyarar dutse na Jinggangshan

cri

Ban da wannan kuma, bajo na marigayi Mao Zedong da kuma kayayyakin da aka kera su bisa kayayyakin gargajiya na juyin juya hali su ma sun jawo hankulan masu yawon shakatawa.

Ba matasa masu kishin tarihi kawai ba, har ma iyaye sun yi jagorar yaransu don ziyarar dutse na Jinggangshan a lokacin hutu. Ban da more idanunsu da kyakkyawan wurare masu ni'ima, suna fatan yaransu za su fahimci tarihin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta hanyar ziyarar dutse na Jinggangshan, ta haka za su kara darajanta zaman rayuwarsu na yau. Mr. Gu Feng, ya ce, 'Na zo dutse na Jinggangshan tare da iyalina a lokacin hutu, da can ina son yarana za su sami ilmin tarihi, a karshe dai dukanmu mun sami ilmin tarihi. Da farko, na fahimci girmar shugaba Mao Zedong, na biyu, na gane cewa, jama'ar kasar Sin sun taba gamuwa da matsaloli da yawa wajen kafuwar Jamhuriya Jama'ar Sin da kuma mulkin kasar Sin da kansu.'

Jama'a masu sauraro, ba a yin zafi sosai a lokacin zafi, kuma ba a yin sanyi sosai a lokacin hunturu a dutse na Jinggangshan, yanayin na da kyau, ya dace da yin yawon shakatawa a duk shekara. Amma ya fi kyau a kai ziyara tun daga watan Afril zuwa watan Oktoba. Saboda a lokacin nan, furannin azalea suke yin toho a ko ina a dutse na Jinggangshan, suna da matukar kyan gani. Yanzu an zabi furen azalea a matsayin fure na birnin Jinggangshan. Bugu da kari kuma, hukumar wurin ta kyautata abincin da jar rundunar sojoji suka ci a lokacin nan, kamar su shinkafa mai launin ja da busasshiyar kabewa, da su zama abinci na musamman. Ban da dandana wadannan abincin musammanm, idan masu yawon shakatawa sun so, za su iya koma gida tare da jan shinkafa da busassun kabewoyi kamar kyauta ga abokai da dangogi.


1  2