Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-24 17:13:57    
Ziyarar dutse na Jinggangshan

cri

Jama'a masu sauraro, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ban da kai ziyara ga shahararrun tsaunuka da koguna da kuma fahimtar al'adun gargajiya na wurin, masu yawon shakatawa da yawa su kan kai ziyara ga wuraren tunawa da juyin juya hali a cikin tarihin zamani na kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani wurin shakatawa mai suna sosai a fannin tunawa da juyin juya hali?sunansa dutse na Jinggangshan.

Dutse na Jinggangshan yana mahadin lardunan Jiangxi da Hunan a kudu maso tsakiyar kasar Sin. Fadin wurin shakatawa na dutse na Jinggangshan ya wuce murabba'in kilomita 200, kuma yawan gandun daji ya wuce kashi 80 cikin dari a nan. A karshen shekaru 1920, saboda dimbin itatuwa a nan, shugaban Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin marigayi Mao Zedong ya kafa sansanin juyin juya hali na farko da ke kauyuka a dutse na Jinggangshan. 'Yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin 'yan juyin mulki sun taka mataki na farko daga dutse na Jinggangshan, a karshe dai sun ci nasara a duk kasar Sin, shi ya sa an mayar da dutse na Jianggangshan tamkar cibiyar juyin juya hali ta kasar Sin. Dutse na Jinggangshan wani dutse ne ga masu yawon shakatawa na yanzu, haka kuma tarihi ne a gare su.

Wurare masu ni'ima fiye da 60 da ke kan dutse na Jinggangshan sun yi suna a gida da waje saboda tsaunuka masu hadari da magangarar ruwa ta musamman da tekun gajimare da furannin azalea masu kyan gani. Dutse na Jinggangshan ya hada da tsaunuka manya da kanana fiye da 500, a cikinsu kuma manyan tsaunuka na Shihou da Wangzhi da Gubai da Yangmei da Guandao da Kongque da Shisun sun fi shahara. Madam Liu Xin wata mai jagorar masu yawon shakatawa da ke aiki a cikin kamfanin yawon shakatawa na duniya na kasar Sin ta yi karin haske kan tsauni na Shihou cewa, (murya ta 1, Liu Xin)

'Masu yawon shakatawa suna tsayawa a kan tsauni na Shihou suna hangen nesa zuwa gabas, akwai wani wuri mai lebur tare da wasu duwatsu a kansa, wadanda suka yi kama da wasu birai. An mayar da wani mafi tsayi da ke cikinsu tamkar mama biri, tana yi wa yaranta jawabi.'

Kamar yadda tsauni na Shihou yake, sauran tsaunuka suna da halin musamman nasu. Ana samun gandun daji na cypress a tsauni na Gubai, shekarun wani mafi tsufa da ke cikinsu ya wuce 800 da haihuwa, dukansu suna kasancewa lami lafiya.

Cikakkun tsoffin gine-gine na juyin juya hali fiye da 100 sun fi jawowa hankulan masu yawon shakatawa. A kusa da wani tsohon asibiti na jar rundunar sojojin kasar Sin na wannan lokaci, wata malama mai suna Yin Qin tana sanya tufafin jar rundunar sojojin kasar Sin na lokacin can bisa gwaji, ta bayyana cewa, 'Ina son sanya wadannan tufafin jar rundunar sojojin kasar Sin na lokacin nan, ina jin zumudi sosai.'

1  2