Birnin Jingdezhen yana arewa maso gabashin lardin Jiangxi da ke a tsakiyar kasar Sin. A nan akwai yumbu mai inganci da ake iya yin amfani da shi wajen yin tangaram. Yau sama da shekaru 1000 da suka wuce, wani sarkin daular Song ta kasar Sin ya ga wani tangaram kyakkyawa da aka fitar a wannan birni, sai ya yi sha'awarsa ainun. Bayan haka ya sa wa birnin suna "Jingde" wato lakabin shekarunsa, abin da ake nufi "Zhen" a cikin Sinanci kuma shi ne birni. Ta haka ana ta kira birnin da suna Jingdezhen.
Tun daga wancan lokaci ne, tangaram da ake yi a birnin sun shahara sosai, ba ma kawai sun zama kayayyaki masu daraja ga sarkuna da sauran manya masu mulki na daulolin gargajiya daban daban na kasar Sin ba, har ma sun zama kayayyaki da suka samu karbuwa sosai, yayin da ake yin ciniki ta hanyar siliki da ake bi a kan teku a zamanin da. Yanzu, a kan ga tangaram kyawawa, kirar birnin Jingdezhen da ake ajiyewa a cikin manyan dakunan nune-nune na kasa da kasa.
1 2 3
|