Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 18:34:55    
Hankalin wadanne kasashe bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta jawo

cri

Yanzu kasar Sin ba ta hako man fetur da yawa daga kasashen Afirka ba, yawan man fetur da kasar Sin ta saya daga kasashen Afirka a yanzu bai kai sulusi na yawan man fetur da kasar Amurka ta saya daga Afirka ba. Ko da yake kasar Sin da kasashen Afirka sun bunkasa cinikin man fetur cikin sauri, amma suna yin ciniki don moriyar juna cikin adalci kuma a fili. Sin da Afirka sun yi hadin gwiwa wajen tattalin arziki da makamashi bisa tushen yin zaman daidai wa daida da taimakon juna bisa matsayin rinjaye da moriyar juna da neman ci nasara tare.

Sa'an nan kuma, cinikin da ke tsakanin Sin da Afirka da kuma kayayyakin masarufi masu inganci da araha sun samar wa 'yan Afirka kayayyakin da suka iya saya, ta haka an daga matsayin zaman rayuwar mutanen wurin. A cikin shekarun nan da suka wuce, matsakacin yawan kasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da ke kudancin hamadar Sahara ya kai misalin kashi 6 cikin dari a ko wace shekara a sakamakon kara yin ciniki da kasar Sin, yankin Afirka da ke kudancin hamadar Sahara ya zama daya daga cikin yankunan da suka fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya.

Har kullun kasar Sin ba ta kutsa kai cikin harkokin gida na sauran kasashe, tana girmama hanyoyin bunkasuwa da kasashen Afirka suka zaba da kansu, ko kusa ba ta nemi ya da hallayenta da tsarin bunkasuwarta a Afirka ba.

Ban da wannan kuma, zargin da kasashen yamma suka yi wa kasar Sin na wai, taimakon da Sin take ba kasashe masu mugun nufi na wai ya samar da cikas wajen ci gaban ayyukan hakkin dan Adam da dimokuradiyya a Afirka ya rasa kan gado a fuskar abubuwan gaskiya.

A gaskiya kuma, babban dalilin da ya sa kasashen yamma su yi furofaganda da gangan cewa, wai kasar Sin tana gudanar da sabon ra'ayin mulkin mallaka a kasashen Afirka, shi ne domin suna damuwa cewa, kasar Sin za ta kawo barazana gare su a fannin moriyarsu a Afirka saboda Sin tana raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka, kuma suna damuwa cewa, mai yiwuwa ne karuwar karfi da tasiri da Sin da Afirka za su bayar a cikin al'amuran duniya za ta kawo kalubale ga tsarin tattalin arziki da siyasa na duniya, wanda kasashen yamma ke shugabanta a yanzu. (Tasallah)


1  2