Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 18:34:55    
Hankalin wadanne kasashe bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta jawo

cri

A kwanan baya, muhimman kafofin yada labaru na kasashen yamma sun ba da labari na wai kasar Sin tana gudanar da sabon ra'ayin mulkin mallaka a kasashen Afirka, haka kuma wasu jami'ai da kwararrun gwamnatocinsu suna son bata dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wata masaniya mai ilmin harkokin Afirka ta cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ta rubuta wani bayanin musamman, inda ta musunta sabon ra'ayin mulkin mallaka na wai.

Kasashen yamma suna ganin cewa, kasar Sin tana gudanar da sabon ra'ayin mulkin mallaka na wai ta hanyoyi 3 a kasashen Afirka. Da farko, suna ganin cewa, kasar Sin ta kara zuba jari zuwa kasashen Afirka don neman samun albarkatun muhimman tsare-tsare, kamar man fetur. Na biyu, suna ganin cewa, kasar Sin tana sayar da kayayyaki masu araha, musamman na kayayyakin sassaka da yawa zuwa kasashen Afirka, wannan ya kawo babbar illa ga bunkasuwar aikin kayayyakin sassaka na wurin, kuma ya sanya masana'antu sun rufe kofarsu, ma'aikata sun rasa aikin yi a wurin. Na uku, kasar Sin tana ya da tsarin bunkasuwar tattalin arzikinta a kasashen Afirka, tana ba da taimako ga kasashe masu mugun nufi na wai ba tare da sharadi ba, ta haka kasashen yamma sun gamu da matsala wajen sa kaimi kan sha'anonin dimokuradiyya da hakkin dan Adam da kuma tafiyar da ayyukan yin Allah wadai da mulkin kama karya da karbar rashawa a Afirka.

A bayyane ne wadannan bayanan da kasashen yamma suka bayar ba su da kan gado bisa tarihi da abubuwan gaskiya. Makasudin kasashen yamma shi ne don yunkurin kiyaye moriyarsu a kasashen Afirka, ba su fatan ganin cewa, kasar Sin tana kara ba da tasiri a Afirka, har ma suna neman hana kasar Sin.

1  2