Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-09 18:50:48    
Aikin koyar da ilmin sana'a na kasar Sin ya samu babban ci gaba cikin sauri

cri

Bayanin da ministan ilmi na kasar Sin Zhou Ji ya yi ya tabbatar da ra'ayin Jiang Jiaji. Ya bayyana cewa, bisa kididdigar da aka yi, yanzu akwai makarantun koyar da sana'o'i kusan 1600 a cikin kasar Sin, kuma a ko wace shekara dalibai fiye da miliyan sun gama karatunsu daga irin wadannan makarantu. A cikin shekarun nan da suka gabata, yawan daliban da suka samu aikin yi bayn sun gama karatunsu daga makarantun koyar da sana'o'i ya fi yawa idan an kwatanta shi da wadanda suka gama karatunsu daga jami'o'i. Ban da wannan kuma Zhou Ji ya ce, "A cikin shekarun nan da suka gabata, yawan daliban da suka samu aikin yi wadanda suka gama karatunsu daga makarantun koyar da sana'o'i yana ta karuwa, har ma yawan wadanda suka gama karatunsu daga makarantun koyar da sana'o'i da yawa bai iya biyan bukatun yawan ma'aikatan da ake nema ba. Shugabannin makarantun masu yawa sun gaya mini cewa, yanzu wasu kamfanoni sun je makarantun domin neman daliban da za su gama karatunsu a shekara mai zuwa." 

Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da gwamnatin kasar Sin ta waiwayi halin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da take ciki yanzu. A cikin shekarun nan da suka gabata, tare da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, shahararrun kamfanonin kasashen duniya sun kafa hukumomin nazari da kera kayayyaki a kasar Sin, a waje daya kuma kamfanonin kasar Sin suna yin kokari domin kara ingancin kayayyaki, duk wadannan abubuwa suna bukatar ma'aikatan da ke rike da fasaha da yawa. Yanzu ba a samu isassun ma'aikatan a fannonin fasahar zamani da gyara motoci ba.

Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin tana ganin cewa, ana iya shigad da fasahohin zamani daga kasashen waje, kuma ana iya yin koyi da sakamako mai kyau wajen gudanarwa daga kasahen waje, amma ba a iya shigad da ma'aikatan da ke rike da fasahohi daga kasashen waje ba, sai a warware matsalar ta hanyar koyar da ilmin sana'o'i.

Mataimakiyar ministan ilmi ta kasar Sin Madam Wu Qidi ta bayyana cewa,"A cikin shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin za ta samar da kudi yuan miliyan 800, kuma gwamnatocin wurare daban daban da makarantun koyar da sana'o'i da kuma mutane na sasan daban daban za su ba da taimakon kudi, ta haka dalibai na makarantun koyar da sana'o'i da yawansu ya kai kashi 20 cikin dari za su samu taimakon kudi. Wannan zai sa kaimi ga kara yawan daliban da makarantun koyar da sana'o'i za su dauka da kuma bunkasa aikin koyar da ilmi sana'a lami lafiya."

Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin shekaru biyar da suka gabata, makarantun koyar da sana'o'i sun samar da dalibai fiye da miliyan 26 ga zamantakewar al'umma, kuma an horar da ma'aikata na birane da kauyuka fiye da miliyan 400, ta yadda aka kyatata ingancin ma'aikata.(Kande Gao)


1  2