Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-09 18:50:48    
Aikin koyar da ilmin sana'a na kasar Sin ya samu babban ci gaba cikin sauri

cri

A cikin shekarun nan da suka gabata, ayyukan koyarwa na kasar Sin sun samu sakamako mai kyau, yawan mutanen da suka shiga jami'o'i don samun ilmi mai zurfi yana ta kara karuwa, sabo da haka Sinawa da yawa suna da zarafin samun ilmi mai zurfi da kuma kara ilminsu. Amma a waje daya kuma, an gano cewa, a cikin kasar Sin, an fi mai da hankali kan ayyukan koyarwa don samun digiri, an yi watsi da aikin koyar da ilmin sana'o'i da kuma kwas din horaswa na fasahohi, har ma ba a iya samu isassun ma'aikatan da suke da ilmi a fannin fasaha ba a wasu wuraren kasar Sin. Yanzu gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai da yawa domin sa kaimi ga bunkasuwar aikin koyar da ilmin sana'a, kuma Sinawa masu yawa suna dora muhimmanci kan aikin koyar da ilmin sana'a.

Jiang Jiaji wata budurwa ce mai shekaru 18 da haihuwa tana koyon zane-zane a kan na'urar kwamfuta a makarantar koyon harkar sadarwa ta birnin Beijing yanzu. Ta gaya wa wakilinmu cewa,"A ganina, za a bukaci mutane da yawa da ke koyon zane-zane nan gaba. A cikin kwanakin nan, malamai na makarantarmu sun ba mu wani aiki, wato yin zane-zane masu motsi kan babban taken 'wasannin Olympics na wayar da kai', daga baya kuma za a zabi wasu nagartattu daga cikinsu domin watsa ta talebijin. Zan shirya wannan flash sosai."

Wakilinmu ya gano cewa, iyaye ba su son tura yaransu zuwa makaratun koyar da sana'o'i kamar makarantar koyon harkar sadarwa ta Beijing, suna ganin cewa, ya fi kyau yaransu su shiga jami'o'i, da kuma shiga hukumomin gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasashen waje bayan sun gama karatunsu.

Jiang Jiaji ta taba nuna damuwa kan sana'ar da ta zaba. Lokacin da ta yi rajistar shiga jarrabawar neman shiga makarantar koyar da sana'o'i, iyayenta ba su amince da wannan shawara da, kuma sun nuna damuwa sosai ga makomarta. Amma iyayenta daga bisani sun canja ra'ayinsu bisa sakamako mai kyau da ta samu wajen karatu a cikin wannan shekara da ta gabata. Kuma abu mafi farin ciki gare ta shi ne dalibai masu yawa da suka gama karatu daga makarantarta sun samu aikin yi cikin sauki. Wasu daga cikinsu kuwa sun zama kusosh a hukumomin da suke ciki ta hanyar ci gaba da kara ilminsu.

1  2