Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-09 18:46:45    
Yin mu'amala tsakanin jam'iyyun Sin da Afirka ya kara sada zumunta a tsakaninsu

cri

Jam'iyyun da ke mulkin kasashen Afirka sun dora muhimmanci kan bunkasuwar tattalin arzikin kasashensu sosai, sun yi kokarin neman yin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma yin hadin kai da kasar Sin wajen tattalin arziki da ciniki, shi ya sa jam'iyyun Sin da Afirka sun yi mu'amala a tsakanin juna a fannin tattalin arziki. A lokacin da shugabannin jam'iyyun kasashen Afirka suke ziyarar kasar Sin, bangaren kasar Sin ya yi kokarin taimake su wajen ganawa da hukumomin kasar Sin da masana'antun Sin da abin ya shafa, ya kuma jagorancinsu ziyarar yankunan Sin da abin ya shafa, ya ba da tallafawa wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsa da kasashen Afirka. Wannan ya karfafa fahimtar juna a tsakanin Sin da Afirka a fuskar tattalin arziki da ciniki, sa'an nan kuma, ya sa kaimi ga bangarorin 2 da su kara yin hadin kai don moriyar juna a sabbin fannoni.

A cikin shekarun nan da suka wuce, a lokacin da take yin mu'amala da jam'iyyun kasashen waje, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta dora muhimmanci kan yin karin haske kan halin da kasar Sin ke ciki da tarihinta, da ci gaban aikin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da gina kanta da kuma manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa domin kasashen Afirka. Yanzu jam'iyyar ta mai da hankali kan yin wa abokan Afirka karin haske kan kafa zaman al'ummar gurguzu mai jituwa, da kuma manufar da kasar Sin ke bi a fannin neman samun bunkasuwa cikin lumana. Ban da wannan kuma, ta gabatar da muhimman takardunta ga kasashen Afirka bisa gayyatar da suka yi mata, ta yadda kasashen Afirka za su kara saninsu kan halin da jam'iyyar da kasar Sin suke ciki.

Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kuma bayyana wa jama'arta karin haske kan Afirka ta hanyar yim mu'amala tsakanin jam'iyyu. Saboda iri wannan mu'amala, jama'ar Sin sun kara saninsu kan Afirka, kuma jam'iyyun kasashen Afirka sun nuna babban yabo.

Saboda kafuwar dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka, tabbas ne Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun kasashen Afirka za su kara yin hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninsu, za su kara samun sakamako da yawa daga wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, jama'ar Sin da Afirka za su kuma kara samun riba daga wajen irin wannan hadin gwiwa.(Tasallah)


1  2