Za a yi taron koli da taron ministoci na karo na 3 na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a nan Beijing, tun daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba na wannan shekara. Yin mu'amala tsakanin jam'iyyun Sin da Afirka, wanda muhimmin bangare ne na dangantakar da ke tsakanin bangarorin 2, ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta da karfafa huldar da ke tsakaninsu.
Yin mu'alama a tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun kasashen waje muhimmin kashi ne na sha'anin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke tafiyar, kuma yana da muhimmanci sosai a fannin harkokin diplomasiyya.
Har zuwa yanzu, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kulla dangantaka tare da jam'iyyu fiye da 60 na kasashe da yankuna fiye da 40 na Afirka, wadanda yawancinsu suke mulkin kasashensu.
Yin mu'amala tsakanin manyan jami'an jam'iyyu muhimmiyar hanya ce da Sin da Afirka suke bi wajen kara amincewa da goyon bayan juna. Tun bayan babban taron Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a karo na 15 har zuwa yanzu, shugabannin kwamitin tsakiya ta jam'iyyar sun yi mu'amala da takwarorinsu na jam'iyyun Afirka, ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya sha aika da kungiyoyin wakilai zuwa ziyarar kasashen Afirka. A gun ziyarar da suka yi wa juna, shugabannin Sin da Afirka sun yi musayar ra'ayoyinsu kan halin da kasashensu ke ciki da sakamako mai kyau wajen kula da harkokin gwamnatocin kasashensu da manyan al'amuran duniya, sun kuma yi tattaunawa kan sabbin hanyoyin da za su bi wajen zurfafa hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu da dangantakar da ke tsakanin kasashe da kuma sabbin fannonin da za su yi hadin gwiwa a kai, ta yadda za su kara fahimta da amincewar juna, da inganta dangantakar sada zumunta ta gargajiya a tsakaninsu, da kuma sa kaimi kan ci gaban huldar da ke tsakaninsu.
1 2
|