Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-04 17:33:34    
Birnin Beijing yana kokarin ba da ilmin Olimpic ga samari da yara

cri

Yanzu yawan makarantun da aka mai da su misalin koyo wajen yin tarbiyyar Olimpic na birnin Beijing ya kai 200. Yayin da Mr. Julian Williams, shugaban makarantar kasashen duniya ta Lecheng ya tabo magana kan abun da wajaba ga yin tarbiyyar Olimpic ya ce, "Wasan Olimpic zai zama wani lokaci mai faranta ran mutanen duniya, kuma zai zama wani lokaci mai kyau ga yaran birnin Beijing cikin zaman rayuwarsu, haka kuma ya zama wani kashi ne daga cikin abubuwan koyo gare mu. Me ya sa ba mu hada tunanin Olimpic da darusanmu? A hakika kuwa suna yin cudanya sosai a tsakaninsu."

Mr. Williams ya kuma bayyana cewa, "Za mu iya hada ra'ayin Olimpic da tunaninsa da kuma tarihinsa da darusanmu, za mu iya hada ra'ayin Olimpic da ilmin lissafi da yanayin halittu da kimiyyar binciken sinadari da likitanci da ilmin dan adam da kuma tattalin arziki, a hakika kuwa duk wadannan ilmi suna hade da tunanin Olimpic sosai."

A karshe, 'yan makarantar kasashen duniya ta Lecheng su ma sun bayyana kyakkyawan fatansu ga wasannin Olimpic na Beijing, yaro Chen Jiawen ya ce, "Ina fatan wasan Olimpic na Beijing zai fi na duk wasannin Olimpic da aka yi a da kyau, wato zai zama wani wasan Olimpic mafi kyau a tarihi." (Umaru)


1  2