Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-04 17:33:34    
Birnin Beijing yana kokarin ba da ilmin Olimpic ga samari da yara

cri

Wasan Olimpic na shekarar 2008 na Beijing yana gaba da zuwa. Wasan Olimpic ba ma kawai ya zama wani gagarumin wasan motsa jiki ba, har ma ya samar da wani zarafi mai kyau domin ba da ilmin al'adun Olimpic ga mutane. Ba da ilmin Olimpic ga yara manyan gobe na birnin Beijing, da gabatar da tunanin Olimpic da darajarsa, da sa kaimi ga wasannin motsa jiki da ake yi cikin makarantu, duk wadannan sun zama daya daga cikin muhimman ayyukan share fage da ake yi domin wasannin Olimpic da na nakasassu na shekarar 2008 na Beijing. Kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing shi ma yana kokari ba tare da kasala ba domin cim ma wannan manufa. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayani game da wannan labari.

Tun bayan da birnin Beijing na kasar Sin ya samu iznin shirya wasannin Olimpic, kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin ya mai da tarbiyyar Olimpic bisa muhimmin matsayi sosai. Yayin da Mr. He Zhenliang, shugaban kwamitin al'adu da tarbiyyar Olimpic na kwamitin Olimpic na kasashen duniya yake amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa ya ce, ba da ilmin Olimpic da yada tunaninsa, ya zama abubuwan da aka tabbatar cikin "yarjejeniyar birni mai shirya wasannin Olimpic" da aka daddale bayan da aka ci nasarar samun izanin shirya wasannin Olimpic a tsakanin kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin Beijing da kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya, kuma ya samar da zarafi mai kyau domin horar da yara mayan gobe na kasar Sin daga duk fannoni.

An ce, kwamitin shiryar wasannin Olimpic na Beijing ya mai da muhimmanci wajen ba da ilmin Olimpic ga 'yan makarantun sakandare da na firamare, a shekarar 2005, kwamitin shiryar wasannin Olimpic na Beijing da ma'aikatar yin tarbiyya ta kasar Sin sun gudanar da "Shirin shekarar 2008 na Beijing" wato ba da ilmin Olimpic ga 'yan makarantun sakandare da na firamare" ta hanyar hadin gwiwa, an yi shirin ba da ilmin Olimpic ga yara manyan gobe wadanda yawansu ya kai miliyan 400 na kasar Sin daga duk fannoni.


1  2