Da can an yi shirin gina babban gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin tare da filin ajiye motoci, wanda fadinsa ya kai murabba'in mita 30,000, amma a karshe dai an gina su dai-dai. An gina wannan filin ajiye motoci a karkashin kasa, inda mutane masu ziyarar filin Tian'anmen suka iya ajiye motoci 1,000 da kuma kekuna 1,400 a ciki. Saboda haka, ajiye motoci da kekuna ba wata matsala ba wadda ke dami mutane.
Mai zanen gine-gine Mr. Paul Andreu, dan kasar Faransa ya yi zanen wannan babban gini bisa salon zamani. Babban gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin gidan wasan kwaikwayo ne mafi girma a duk kasar Sin, ya kuma yi suna ne domin an iya nuna wasannin kwaikwayo da kuma shirye-shiryen da suka shafi fasaha iri daban daban a nan. Yanzu yana yin zaman daidaituwa tare da sauran gine-gine a filin Tian'anmen, yana jiran masu yawon shakatawa. 1 2
|