A cikin shirinmu na yau, da farko dai za mu gabatar muku da wasu abubuwa kan babban gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin da ke nan Beijing, daga baya kuma sai wani bayanin musamma mai lakabi haka 'Jin dadin zaman rayuwar masunta a birnin Yuyang na lardin Shandong'. Babban gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin yana yammacin babban dakin taro na jama'a a tsakiyar birnin Beijing. An yi shekaru 4 ana gina shi tun daga ran 12 ga watan Disamba na shekarar 2001 har zuwa shekarar 2005. An yi wasu kwaskwarima don rage kudin ginawa da kuma fadinsa. Ta haka a karshe dai an yi amfani da dalar Amurka miliyan 325 wajen gina wannan babban gidan wasan kwaikwayo a maimakon dalar Amurka miliyan 362 da aka yi shirin yin amfani da shi. Babban dalilin da ya sa raguwar kudin ginawa shi ne rage fadinsa.
Babban dakin wasar kwaikwayo ta waka da ke cikin babban gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin yana da kujeru 2,500, inda shahararrun kungiyoyin wasar kwaikwayo ta waka da na rawar ballet na kasa da kasa su kan nuna shirye-shirye masu kayatarwa. Makada su kan yi kida da wake-wake iri na kasashen yamma da iri na gargajiya na kasar Sin a cikin babban dakin kida da wake-wake, wanda ke da kujeru 2,000. Ban da wannan kuma, akwai wani gidan wasan kwaikwayo a cikin wannan babban gini, inda a kan nuna wasan kwaikwayo na zamani da wasar kwaikwayo ta waka ta Peking wato Peking Opera a Turance da sauran wasannin kwaikwayo na waka na kasar Sin da kuma ma'adanin hotonan zane.
1 2
|