Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-26 17:58:33    
Kasar Sin tana kokarin kiyaye al'adun kananan kabilun kasar

cri

Mr.Tondrup Wangden ya ce, yanzu kasar Sin ta riga ta dauki matakai da dama wajen kiyaye al'adun kananan kabilu, kuma ta hanyar zuba kudade da aiwatar da shirye-shirye da gwamnatin tsakiya da kananan hukumomi suke yi, kasar Sin ta sami wasu nasarori a wajen kiyaye al'adun kananan kabilunta. Amma duk da haka, ana ci gaba da fuskantar wasu matsaloli a wajen kiyaye al'adun kananan kabilu a halin yanzu, misali ba a bunkasa da kuma yi amfani da al'adun kananan kabilun kasar Sin sosai ba, kuma ba a zuba isassun kudade wajen kiyaye al'adun kananan kabilu ba.

Game da wadannan matsaloli, jami'in nan ya ba da shawarar cewa, nan gaba, ya kamata kasar Sin ta kara zuba kudade ga harkokin al'adun kananan kabilu, musamman ma ga wasu sassan kula da harkokin kananan kabilu ko kuma hukumomin al'adu da ke shiyyoyin kananan kabilu masu cin gashin kansu, kuma kamata ya yi a kara zuba kudade gare su a wasu lokuta na musamman.

Ban da wannan, malam Tondrup Wangden ya kuma fayyace cewa, a halin yanzu dai, kwamitin kula da harkokin kabilun kasar Sin yana tsara wani shiri dangane da bunkasuwar kananan kabilu nan da shekaru biyar masu zuwa, wanda ke shafar ayyuka da dama na kiyaye al'adun kabilu.

A sa'i daya kuma, Mr.Tondrup Wangden ya kuma sa kaimi ga yankunan kananan kabilu da su yi amfani da albarkatunsu na al'adu, su bunkasa harkar al'adu, har sun sa ta zama wani madogari na tattalin arziki. A ganinsa, ta wannan hanya, ba ma kawai za a cimma burin kiyaye al'adun kabilu ba, hatta ma za a iya ingiza bunkasuwar tattalin arzikin yankunan kananan kabilu. (Lubabatu)


1  2