Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-26 17:58:33    
Kasar Sin tana kokarin kiyaye al'adun kananan kabilun kasar

cri

A jiya ranar 25 ga wata, a nan birnin Beijing. An kawo karshen wasannin nune-nunen fasahohin kananan kabilun kasar Sin na karo na uku. A cewar wani jami'in kula da harkokin kabilu na kasar Sin, arzikin fasahohin kabilu iri daban daban da aka nuna a cikin wasannin, ya bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu a wajen kiyaye al'adun kananan kabilu. A nan gaba, kasar Sin za ta kara kokartawa wajen kiyaye da kuma bunkasa al'adun musamman na kananan kabilu.

Kasar Sin kasa ce da ke da kabilu da dama. Ban da kabilar Han, akwai kuma sauran kananan kabilu 55. Wadannan kabilu dai suna da al'adunsu na musamma wadanda ke sha bamban da na sauran kabilu. Wadannan al'adun da aka bayar da su daga zuriya zuwa zuriya, cike suke da hikimomin kabilu daban daban na kasar Sin. Amma a yayin da al'adun wasu kabilu ke daukar abubuwa nagari daga al'adun sauran kabilu a cudanyar da suke yi, halayensu na musamman sun kuma sha tasiri. Sabo da haka, har kullum, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan kiyaye da kuma bunkasa al'adun gargajiya na kananan kabilu.

Kwanan baya, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kabilu na kasar Sin, Tondrup Wangden ya bayyana a gun wani taro cewa, ko a cikin dokokin kasar Sin ko kuma a cikin manufofinta, akwai bayanai dangane da kiyaye al'adun kananan kabilu. Ya ce, 'A fili ne tsarin mulkin kasar Sin da dokar cin gashin kansu a shiyyoyin kananan kabilu da dai sauran dokokin kasar suka bayyana cewa, ya kamata a girmama al'adun kabilu daban daban da tallafa wa bunkasuwar al'adun musamman na kananan kabilu. Ko wace kabila tana da 'yancin bunkasa da kuma yin amfani da babbakunta, kuma tana da 'yancin kiyaye da gyaran al'adunta, tana kuma da 'yancin bin addinin da take ga dama.

1  2