Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-21 18:34:07    
Bayyanin kan birnin Tianjin

cri

Mr. Ning , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin Ya yi nuni da cewa , a wajen kiyaye ikon musamman na lambobin kasuwanci da aka rajista , Birnin Tianjin tana mai da hankali sosai kan lambobin kasuwanci na kasar Sin da na kasashen waje .

Ya kuma bayyana cewa , A cikin aikin mun kara karfin musamman don kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasashen waje .

Mr. Ning ya bayyana cewa , a cikin shekaru 5 da suka shige , mun dauki aikin kiyaye shahararrun lambobin kasuwanci na kasashen waje kamar wani muhimmin aiki na bnirnin Tianjin na kasar Sin . Musamman ma daga shekarar 2004 zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara , Ofishin lambobin kasuwanci da Kwamitin duba lambobin na hukumar sun yi amincewa da shahararrun lambobin kasuwanci guda 30 na kasashen waje .

Kasar Sin tana daya ce daga cikin kasashe masu fama da lambobin jebu a duniya . Bayan da aka shiga sabon karni , kasar Sin ta dauki matakan magance laifufkan kera lambobin jebu .

A gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 15 ga wata a nan birnin Beijing , Li Dongsheng , shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin ya ce , kasar Sin ta yi na'am da wadannan shahararrun lambobin kasuwanci kuma tana kiyaye ikon mallakar ilminsu , ta sami yabo sosai daga masana'antu masu yawa musamman ma wasu manyan kamfanonin ketare kuma sun karfafa amincewar aikin kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasar Sin . Saboda haka , kasar Sin ta jawo hankulan kasashe masu yawa su zo nan kasar Sin don rajista lambobinsu . Mu ma haka , birnin Tianjin zai aiwatar da manufar gwamnatin kasar Sin , kuma za mu mai da hankali sosai kan kananan fannoni .

Mr. Li , kakakin watsa labaru na Kamfanin ba da wutar lantarki na Tianjin ya bayyana cewa , tun daga watan Satumba na shekarar bara , kamfaninsa ya fara aikin share fage don samar da wutar lantarki a wannan shekara .

Mr. Li ya ce , gwamnatin birnin Tianjin ta tattara kudin RMB fiye da yuan biliyan 2 don kyautata manyan ayyukan ba da wutar lantarki , kuma a kafin ran 30 ga watan Yuli na wannan shekara mun gama ayyukan . A yanayin zafi , ayyukan sun ba da amfani kwarai da gaske .

Ban da birnin Tianjin , hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin da sauran wurare su ma sun yi aikin share fage sosai don ba da wutar lantarki mai yawa a yanayin zafi . A watanni 6 na farko na wannan shekara , Kamfanin ba da wutar lantarki na birnin Tianjin ya gina manyan hanyoyin ba da wutar lantarki na kilomita fiye da dubu 5 . Ta haka an kara karfin samar da wutar lantarki .

A wajen samar da wutar lantarki , wurare daban daban na birnin Tianjin na kasar Sin suna bin wata manufar cewa , da farko dai za a samar da wutar lantarki ga zaman yau da kullum na jama'a . Sa'an nan kuma ga masana'antu da aikin noma da sauran sana'o'i .  (Ado).


1  2