Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-21 18:34:07    
Bayyanin kan birnin Tianjin

cri

Birnin Tianjin yana daya daga cikin manyan birane 4 dake karkashin gwamnatin kasar Sin wato Beijing da Shanghai da Tianjin da Chongqing . Birnin Tianjin yana gabar tekun dake arewacin kasar Sin . Kullum ana kiransa cewa lu'u-lu'u mai haske a Tekun Bohai . Fadin birnin Tianjin ya kai muraba'in kilomita dubu 11 da 919 .

Birnin Tianjin yana da unguwoyi guda 15 da gundumomi guda 3. Wato Unguwar Heping da Hedong da Nankai da Hexi da Hebei da Hongqiao da Tanggu da Hangu da Dagang da Dongli da Xiqing da Jinnan da Beichen da Wuqing da Baodi da Gundumar Jinghai da Ninghe da Gundumar Ji .

Birnin Tianjin yana da wadatattun albarkatai . Fadin gonakai ya kai muraba'in kadada dubu 485 , wato ya kai kashi 40.7 cikin 100 na duk fadin birnin . A yankin Binhai akwai sauruka mai fadin muraba'in kilomita fiye da 120 . A wurin nan za a iya bunkasa masana'antun man fetur da masana'antun kera magunguna .

Abin da kuka saurara dazu nan shi ne labarin kasa kan birnin Tianjin . yanzu bari mu yi 'dan bayani kan makamashin birnin . Kwanan baya gwamnatin birnin Tianjin ya kira taron aiki kan yadda za a yi tsimin makamashi . Zhang Lichang , wakilin Ofishin siyasa na Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin kuma sakataren Kwamitin jam'iyyar Tianjin da Dai Xianglong , shugaban birnin Tianjin sun yi jawabi kan aikin tsimin makamashi . Mr. Dai ya jaddada cewa , za mu yi kokari don mai da birnin Tianjin da ya zama birni mai tsimin makamashi kuma mai kasance da muhalli mai kyau da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci . Shugaban birnin ya karfafa magana cewa , kwamitin jam'iyyar Tianjin da gwamnatin Tianjin sun tsai da kudurin cewa , za a rage yawan makamashin da za a yi amfani da su har zuwa kashi 20 cikin 100 . Dole ne masana'antu daban daban da hukumomi daban daban na gwamnatocin matakai daban daban su tabbatar da wannan kudurin a cikin manyan kamfanoni masu yin amfani da makamashi mai yawa .

Yang Dongliang , mataimakin shugaban birnin Tianjin shi kuma ya yi jawabi , inda ya bayyana cewa , A ran 14 ga watan Agusta a nan birnin Tianjin , An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar birnin Tianjin ta 10 . Taron ya zartas da Shirye-shiryen raya tattalin arzikin birnin da zaman al'umman Tianjin a shekaru 5 masu zuwa da rahoton aikin gwamnati .

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin birnin Tianjin na shekara-shekara zai kai kashi 9.5 cikin 100 . Kuma an tabbatar da makasudin rage yawan makamashin da za a yi amfani da rage yawan gurbatattun abubuwan da za a fitar . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kafa sababbin kauyyuka da hanzarta gyare-gyaren tattalin arziki da ciyar da yalwatuwar unguwoyi da gundumomi cikin daidaici , za su zama tsarin musamman da manyan ayyukan birnin Tianjin .

Mr. Yang ya ce , a birnin Tianjin za a kau da haramtattun aikace-aikacen cinikin litattafai da faye-faye masu satar ikon mallakar ilmi .

Ning Wanglu , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin ya bayyana cewa , tun daga farkon wannan shekara sassa daban daban na Hukumar ta riga ta yi binciken al'amuran keta ikon lambobin kasuwanci .

1  2