Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 18:05:12    
Ana gudanar da aikin gina muhimman filayen wasannin Olympic na Beijing lami-lafiya

cri

A zahiri dai , yin amfani da irin wannan sabon kaya mai yawan gaske, wani halin musamman ne na aikin gina filin wasa mai siffar ' Gidan Tsuntsu'. Injiniya Li Jiulin ya kara da, cewa lallai ana shan wahala wajen gina wannan filin wasan mai kayatarwa. Dalili na farko, shi ne an yi kasafin musamman ga wannan babban aiki ,wato ke nan ana bukatar yin amfani da sabbin fasahohi wajen gina filin wasan da bakar karfe da kuma leda mai haske kuma mai kama da gilashi. Don haka, babun abin da ya cancanci ya zama darasi da aka samu daga muhimman ayyukan da aka yi a da; Dalili na biyu, shi ne irin wannan kasafin musamman da aka yi ya sa aka kasa samo abubuwan shaidawa a fannoni da dama lokacin da ake yin kasafi ,da ginawa da kuma sa ido kan ingancin filin wasan.

Yanzu, ma iya cewa, yunkurin gina wannan babban filin wasan mai siffar ' Gidan Tsuntse', yunkuri ne da ake yi na kawar da dimbin wahalhalun da aka sha. Masu aikin gina wannan filin wasan sun sha yin gwaje-gwaje da kirkiro sabbin kayayyaki ta hanyar kimiyya da fasaha har sun warware dukkan maganganu masu wuya, a karshe dai sun mayar da takardar zane don ta zama hakikanin abu wato filin wasa mai kayatarwa.

A cikin wannan yunkurin, ma'aikata masu dimbin yawa na kasar Sin sun kirkiro sabbin kayayyaki ba tare da tsangwama ba. Nauyin kananadadden karfe da aka yi amfani da su wajen gina wannan filin wasa mai siffar ' Gidan Tsuntsu' ya kai Ton 42,000 wadanda aka kera su cikin gidan kasar; Kuma wani irin kananadadden karfe daga cikinsu, wani kaya ne da ya fi karfin sauran kayayyakin gine-gine a duniyar yau, wato ke nan irin wannan kaya mai fadin murabba'in mm. daya na iya daukar kaya mai nauyin kilo 46.

Nan da shakera daya da 'yan watanni masu zuwa, za a harhada kayayyaki da injuna a cikin wannan filin wasa. Idan an kammala aikin gina shi kwata-kwata, to zai iya daukar 'yan kallo da yawansu ya kai 91,000, wanda kuma zai zama filin wasa mafi girma a kasar Sin.

Ana sa ran alherin, cewa filin wasannin motsa jiki mai siffar ' Gidan Tsuntsu' zai janyo hankulan mutanen duk duniya yayin da ake yin bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 a cikinsa; A wancan lokacin, za a kara samun wani babban gini mai kayatarwa a nan birnin Beijing. ( Sani Wang )


1  2