Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 18:05:12    
Ana gudanar da aikin gina muhimman filayen wasannin Olympic na Beijing lami-lafiya

cri

Kimanin shekaru biyu ke nan da suka yi saura don gudanar da bikin bude taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a ran 8 ga watan Agusta na shekarar 2008. Yanzu ana tafiyar da aikin gina muhimman filaye da dakuna na wasannin motsa jiki na Olympic da kyau, wanda yake kan matsayin muhimman ayyukan share fage ga shirya taron wasannin Olympic. Kwanakin baya, kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing ya shelanta, cewa za a kammala aikin gina dukan filaye da dakunan wasannin Olympic kafin karshen watan Yuli na shekara mai zuwa.

Filin wasan motsa jiki na kasa, muhimmin filin wasa ne inda za a gudanar da bikin bude taron wasannin Olympic na Beijin a shekarar 2008 da kuma na rufe shi. Ana kiran wannan filin wasa ' Gidan Tsuntsu' saboda siffarsa ta yi kama da gidan tsuntsu ne. A matsayin wani filin wasannin motsa jiki mafi kayatarwa, an soma gina shi ne a karshen watan Disamba na shekarar 2003 a wurin dake cikin lambun shan iska na Olympic a arewancin birnin Beijing. Yanzu, ana gudanar da aikin gina shi daidai bisa tsarin da aka yi. Mataimakin babban injiniya Mr. Li Jiulin ya bayyana, cewa: ' Ya zuwa ran 15 ga watan Nuwamba na shekarar bara, an kammala aikin gina dakalin 'yan kallo da sumunti; kuma a ran 15 ga watan Satumba na shekarar bara, an soma gina wannan filin wasa da bakin karfe. Kawo yanzu dai, an riga an kamala kashi 80 cikin l00 na aikin gina marufin filin wasan da bakin karfe. Ana sa rai, za a kammala aikin gina shi kafin karshen shekarar da muke ciki. Dukkan ayyukan da muke yi suna dacewa da bukatun sassan da abun ya shafa'.

Jama'a masu sauraro, idan kun samu damar zuwan nan Beijing, to za ku iya ganin wannan gagarumin filin wasannin motsa jiki mai siffar ' Gidan tsuntsu' . Injiniya Li Jiulin ya kuma bayyana, cewa aiki na nan gaba da za su yi, shi ne rufe filin wasan da wata leda mai haske kuma mai kama da gilashi, wadda aka kera ta ta hanyar kimiyya da fasaha ta zamani. Irin wannan leda mai kama da gilashi ta kuma iya tare ruwa da riga-kafin kura. Wannan sabon kaya ba safai akan ga irinsa ba a duniya sai dai an gan shi ne a babban filin wasa na Munich na kasar Jamus.

1  2