Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 17:52:02    
Lardin Fujian na kasar Sin yana shirin sake gaggauta bunkasa tattalin arzikinsa

cri

A sakamakon ci gaba da ake samu wajen gina tashoshin jiragen ruwa da sauran manyan ayyuka, lardin Fujian ya jawo makudan kudaden jari daga wajen 'yan kasuwa na Taiwan. Malam Sun Dahai, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin sabon yankin masana'antu na zamani na birnin Xiamen na lardin Fujian ya bayyana cewa, "yawan kudi da wani babban kamfanin yin monitor na zamani mai suna "Youda" na Taiwan ya zuba wajen kafa masana'antun yin irin wannan monitor a yankin nan zai kai dalar Amurka miliyan 500. Bayan aka kammala aikin gina wannan masana'antu, yawan kudi da za a samu daga wajensa zai kai kudin Sin Yuan biliyan 40."

Ban da wannan kuma, 'yan kasuwa na Taiwan da yawa suna kara zuba kudaden jari wajen gudanar da aikin gona a lardin Fujian, sabo da yanayin lardin nan ya tashi kusan irin daya da na Taiwan. Malam Xu Ciyan, dan kasuwa na Taiwan wanda ya zuba jari wajen noman wani irin fure da ake kira Orchid a Turance a filin gonaki da fadinsu ya kai muraba'in mita dubu 14 a lardin Fujian, ya bayyana cewa, "a Taiwan ana yin aikin noma ta hanyar zamani. Amma a baban yankin kasar Sin kuma ana yin aikin noma ne ta hanyar gargajiya. Sabo da haka idan babban yankin ya shigo da hanyar zamani da ake bi daga Taiwan, ya gyara amfanin gona sosai, to, manomansa za su ci gajiyar hanyar nan sosai." (Halilu)


1  2