Lardin Fujian yana bakin teku da ke a kudu maso gabashin kasar Sin, kuma ta gefen teku, yana fuskantar tsibirin Taiwan na kasar. Yau sama da shekaru 20 da suka wuce, lardin nan ya kasance cikin sahun gaba a kasar Sin wajen gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Ya taba jawo makudan kudaden jari daga wajen 'yan kasuwa na kasashe da yankuna daban daban, bisa matsayinsa mai rinjaye na dab da Taiwan da Hong Kong da Macao. Amma daga baya ya yi baya-baya wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin, idan an kwatanta shi da lardin Guangdong. Alal misali, jimlar kudi da lardin Guangdong ya samu daga wajen samar da kayayyaki ta wuce kudin Sin Yuan biliyan 2100 a shekarar 2005, amma jimlar kudin nan da lardin Fujian ya samu ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 650 kawai. Ka zalika yawan kudin jari da 'yan kasuwa na Taiwan suka zuba a lardin Fujian ma bai kai na lardin Guangdong ba.
Malam Yan Zheng, shugaban cibiyar nazarin ilmin zaman rayuwar yau da kullum ta lardin Fujiang ya bayyana cewa, "lardin Fujian lardin babban yankin kasar Sin ne da ya fi kasancewa daura da Taiwan. Amma jama'ar Taiwan ba su iya zuwa lardin Fujian kai tsaye ba, kuma ba su iya jigilar kayayyakinsu zuwa lardin daga Taiwan kai tsaye ba, sai su bi ta Hong Kong. Dalilin da ya sa haka shi ne domin hukumar Taiwan na kawo cikas. Ta haka yawan kudi da 'yan kasuwa na Taiwan ke kashewa wajen zuba jari ya karu. A cikin irin wannan hali ne, 'yan kasuwa na Taiwan sun fi sha'awar zuba jarinsu a lardin Guangdong wanda ke dab da Hong Kong. "
Malam Yan Zheng ya kara da cewa, wani babban dalilin da ya sa aka bunkasa tattalin arzikin lardin Fujian sannu sannu, shi ne domin lardin ya yi baya-baya wajen yin manyan ayyuka. Amma abin mai faranra rai shi ne, yanzu lardin Fujian yana kokartawa wajen gina tashoshin jiragen ruwa a gabar yammacin yankin tekun Taiwan, don gaggauta bunkasa harkokin tattalin arzikinsa. Tsawon bakin teku na lardin Fujian ya wuce kilomita 3300, wato ya kai matsayi na biyu a duk kasar Sin. An ruwaito cewa, ya zuwa shekarar 2010, nauyin kayayyaki da za a shiga ko fitar daga tashoshin jiragen ruwa na lardin zai wuce Tan miliyan 300 a ko wace shekara.
1 2
|