Ban da wannan kuma, ana cin gajiyar tasoshin Internet wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a yankunan karkara da ke kewayen birnin Beijing. Malam Wang Fenglei, manajan babban kamfanin sadarwa mai suna Hengxin na birnin Beijing ya ce, "ana iya watsa labarun ga 'yan birnin kan wuraren da za su yi yawon shakatawa a karkarar birninsu ta hanyar tashoshin Internet, ta haka masu yawan shakatawa da ke zuwa wadannan wurare za su karu, sa'an nan kuma yawan kudin shiga da manoma ke samu ma zai karu."
Alal misali, a farkon shekarar nan, wuraren yawon shakatawa biyu na yankin Pinggu da ke zagayen birnin sun tallata wurarensu na yawon shakatawa ta hanyar Internet, ta haka yawan mutane da suka yi yawon shakatawa a wuraren biyu ya karu zuwa kimanin 9000 a lokacin hutu na ranar bikin ma'aikata na duniya, yawan kudin shiga da wuraren biyu suka samu ma ya wuce kudin Sin Yuan dubu 240.
Malam Yang Baozhu, masanin ilmin sadarwa na kasar Sin ya fayyace cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta kashe makudan kudade wajen yin manyan ayyukan sadarwa da horar da kwararru, ta yadda za a kara daga matsayin kimiyya da fasaha a kauyukan kasar Sin. (Halilu) 1 2
|