Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-01 16:44:01    
Ana bunkasa kauyukan kasar Sin tare da taimakon fasahar sadarwa

cri

Daga cikin mutanen Sin da yawansu ya kai biliyan 1.3, akwai sama da mutane biliyan 800 wadanda ke zama a kauyuka. Sabo da haka bunkasa aikin noma da kyautata matsayin zaman rayuwar manoma sun zama manyan ayyuka da gwamnatin kasar Sin ke yi a kullum. A sakamakon ci gaba da aka samu wajen gudanar da ayyukan sadarwa a kasar Sin a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, an yi ta samar da taimako ga bunkasa aikin noma a kauyukan kasar.

An ruwaito cewa, yanzu, masana'antu da yawa suna nan suna kokari sosai wajen fitar da sabbin kayayyakinsu da fasaharsu ta sabon salo zuwa kauyuka da ke karkarar birnin Beijing, don taimakon manoma wajen bunkasa aikin noma. Tun daga shekarar bara, aka fara gudanar da wani aiki musamman domin daga matsayin sadarwa a wadannan kauyuka. Bisa shirin da aka yi, za a kafa gidajen sadarwa misalin 300 wadanda za su samar wa manoman labaru ta hanyar Internet. Madam Liu Guiying, wata manomiya ce da ke zaune a yankin Pinggu da ke a karkarar birnin Beijing ta bayyana cewa, yanzu mu monoma muna samun bayanai cikin sauki a kan labarun aikin noma da na kasuwanci daga na'ura mai aiki da kwakwalwa ta hanyar Internet. Ta gwada misali cewa, "idan manoma suna son sayar da wani irin 'ya'yan itatuwa da ake kira Pear a Turance, to, za su iya samun labarun kasuwanni ta hanyar Internet don sayar da su bisa farashi mai kyau. Ta haka manoma za su sami kudin shiga mai yawa. Haka kuma yayin da manoma za su sayi injunan gyara amfanin gona, sai su nemi labarun da abin shafa ta hanyar Internet don sayen injunan nan masu inganci bisa farashi mai rahusa."

Wani babban kamfanin sadarwa mai suna Hengxin na birnin Beijing ya riga ya gina tashohin Internet da yawansu ya kai 36 a karkarar birnin Beijing. Malam Fu Bin, mataimakin babban manajan wannan kamfani ya bayyana cewa, yanzu, manoma suna sayar da amfanin gonansu zuwa ga 'yan kasuwa kai tsaye ta hanyar tashar Internet, ta haka dai ne yawan kudin shiga da suke samu daga wajen sayar da amfanin gonansu ya kan karu. Ya kara da cewa, "mun gina tashoshin Internet a kauyuka ne domin taimaka wa manoma wajen samun labaru iri daban daban kan amfanin gona da ake sayarwa a kasuwanni, ta yadda za su sayar da amfanin gonansu zuwa ga 'yan kasuwa kai tsaya ba ta hannun dallalai ba."

1  2