Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 20:48:29    
Birnin Beijing

cri

Jimlar GDP Wato kudin da aka samu daga aikin kawo albarka na birnin Beijing a shekarar 2004 ta kai kudin Sin wato Yuan biliyan 428.33, jimlar kudin da aka samu wajen kayayyakin shigi da fici ta kai dala biliyan 94.66, yawan sabbin ayyukan da aka yi ta jarin musanya ya kai 1806, yawan kudin da aka samu wajen tafiyar da kwagiloli ta hanyar jarin musanya ya kai dala biliyan 6.26.

Yawan mutanen birnin Beijing da suka sake samun aikin yi a shekarar 2004 ya kai dubu 174.3. Yawan mutanen da suka sayi inshorar tsufa ya kai miliyan 4.84. Yawan kudin da mutanen birnin Beijing suka ajiye cikin Bankuna a shekarar 2004 ya kai Yuan biliyan 612.23. Matsakaicin fadin gidajen mazaunan birnin da na garuruwa ya kai murabba'in mita 19 da wani abu.

Birnin Beijing babban magamin zirga-zirgar hanyoyin jiragen kasa da na sama na fasinja ne, a can akwai hanyoyin dogo da suka hada birnin nan da biranen Guangzhou da Jiulong da kuma Shanghai, har sun kai ko'ina na duk kasa baki daya. Sha'anin waya da aike- aike shi ma yana samun bunkasuwa da sauri. Yawan kudaden da aka samu ashekarar 2004 wajen zirga-zirga da sufuri ya kai Yuan biliyan 14.88 Yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a duk shekarar ta hanyar jiragen sama ya kai ton dubu 569, yawan fasinjojin da aka yi gigilarsu kuma ya kai miliyan 16 da dubu 927.

Yawan sassan kimiyya da fasaha da ake da su ya kai 4000 a duk birnin Beijing wadanda suke da mutane dubu 290 masu binciken kimiyya da fasaha. Yawan kudaden da aka ware domin binciken kimiyya da fasaha ya kai Yuan biliyan 51. Yawan jami'o'I da kwalejojin da ake da su yanzu ya kai 77 a wannan birnin, yawan daliban da suke dauka kuma ya kai dubu 147.

Yawan sassan nuna sinima da ake da su ya kai 172 a duk birnin Beijing, fadin wuraren da suke iya sauraran rediyo da kallon Telebijin ya kai kashi 99.5 bisa 100.

Fadin wuraren da ake tafiyar da tsarin likitanci bisa turken gama karfi kuma bisa matakin gundumomin kauyuka ya kai kashi 100 bisa 100 a duk birnin, wato yawan manoman da suke tafiyar da wannan sabon tsarin likitanci ya kai miliyan 2.3.

Mu'amalar da ake yi tsakanin birnin Beijing da kasashe da shiyyoyi daban-daban na duniya wajen tattalin arziki da ciniki da kimiyya da fasaha da aikin ba da ilmi da al'adu sai kara yawa suke a kowace rana. Ana nan ana ta kai da kawowa cikin zumunci a tsakanin birnin Beijing da gwamnatoci da jama'a da kungiyoyin zaman al'umma.

Ya kasance da dangantakar aminci a tsakanin birnin Beijing da hedkwatoci da sauran manyan birane 124 na kasashe 72. Yanzu da akwai ofishoshin jakadu 137 na kasashen waje da ke nan birnin Beijing, yawan daliban da suke dalibci a nan kuma ya kai fiye da dubu 17. Birnin Beijing kuma ya taba samu nasara wajen shirya wasannin motsa jiki na 11 na Asiya, da babban taro na 4 na matan duniya da sauran manyan tarurrukan kasashen duniya. Wani muhimmin aikin da ake yi yanzu a nan birnin Beijing shi ne yin kokarin share fage domin wasannin Olimpic na 29 da za a yi a shekarar 2008 a nan birnin Beijing na kasar Sin. (Umaru)


1  2