Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 20:48:29    
Birnin Beijing

cri

Birnin Beijing hedkwatar Jamhuriyar jama'ar Sin ne, yana arwacin babban filin karkara na arewacin kasar Sin, shi ne cibiyar siyasa da al'adun kasar, kuma yana daya daga cikin cibiyoyin yin mu'amala tsakanin kasashen duniya, kuma birnin ne da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye, shugaban birni na yanzu shi ne Wang Qishan. Duk fadin birnin Beijing ya kai murabba'in kilomita 16,800, kuma yana hade da jihohi 12 da gundumomi 6, jimlar mutanen birnin ta kai miliyan 14 da dubu 927, kuma yana hade da dukkan kabilun da ake da su a kasar Sin wadanda yawansu ya kai 56, ban da kabilar Han kuma, sauran kabilu kamar kabilar Hui da Man da Mongoliya wadanda yawan mutane na kowanensu ya wuce miliyan daya.

Birnin Beijing yana yanki mai matsakaicin zafi da sanyi, kuma maras fari da damshi sosai, matsakaicin yawan zafi da akan samu ya kai digiri 13 a kowace shekara, matsakaicin yawan ruwan sama da aka yi kuma ya kai millimita 507.7 a kowace shekara.

Birnin Beijing wurin mahaifa na mahahuran "mutanen zamanin jahiliyya na Beijing" ne, bisa takardun da kayayyakin tarihi da aka bincika an ce, yau da shekaru fiye da 3000 ke nan da aka kafa wannan birni, kuma ya taba zama hedkwatar sarakunan gargajiya na dauloli 5 wato daular Liao da Jin da Yuan da Ming da kuma Qing. An kafa Jamhuriyar jama'ar Sin a ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, daga nan ne birnin Beijing ya zama hedkwatar Jamhuriyar jama'ar Sin, kuma ya zama cibiyar siyasa da al'adu ta kasar Sin, da cibiyar yin zirga-zirga tsakanin kasashen duniya. M.D.D. ta shigar da wurare masu ni'ima na birnin Beijing ciki har da fadar sarakunan gargajiya da babbar ganuwa da tsohon wurin zaman mutane na zamanin jahiliyya na Zhoukoudian.

Birnin Beijing yana da sassan masana'antu iri-iri, ciki har da masana'antar harhada magunguna, da kayayyakin al'adu da ba da ilmi da fasaha, da masana'antar kera kayayyakin lantarki da yin sakakkun kayayyaki da kayayykin masana'antu da kayayyakin gida masu aiki da lantarki wadanda suka kama sahun gaba na duk kasa. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sana'o'in yawon shakatawa da kasuwanci da kudi da sadarwa na birnin Beijing sun ma sun samu ci gaba da sauri, kuma sun sa birnin ya zama daya daga cikin kasuwannin saye da sayarwa da tashoshi mafiya girma wajen kayayyakin shigi da fici na duk kasa baki daya, muhimman hajjojin da aka fitar da su daga birnin Beijing su ne kayayyakin saka da tufafi da darduma da kayayyakin kere-kere da kayayyakin lantarki da hatsi da man girki da kayayyakin musamman na wurin.

1  2