Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 16:45:19    
Wani jarumin kasar Sin na zamanin da mai suna Qi Jiguang

cri

Qi Jiguang ya takaita fasahohin da aka samu wajen yaki da 'yan fashin teku na kasar Japan cewa, dalilin da ya sa sojojin daular Ming suka gaza cin nasara wajen yaki da 'yan fashin teku na kasar Japan shi ne saboda ba su da karfin yaki, bisa sakamakon nan ne ya tattara sojoji daga wajen jama'a , sa'anan kuma ya horar da su, shi kansa ya kafa wata rundunar sojojin ruwa, an kira rundunar nan da cewa, "sojojin gidan Qi", daga nan, sai sojojin gidan Qi suka yi ta samun nasara wajen yaki da 'yan fashin teku na kasar Japan ba tare da kowace hasara ba, sun yi suna a duniya.

Alal misali, a shekarar 1561, 'yan fashin teku na kasar Japan da yawansu ya kai dubu 10 ko fiye sun kai farmaki kan shiyyar Taizhou na lardin Zhejiang na kasar Sin, sai nan da nan sojojin gidan Qi suka tashi tsaye suka shiga cikin yaki da 'yan fashin, amma 'yan fashin sun yi makarkashiya a boye sosai, sun yi watsi da kayayyakin zinariya da sauran kayayyaki masu daraja sosai a kan hanyoyin da suka ratsa, amma sojojin gidan Qi suna da da'a sosai, kuma sun bi dokokin da aka tsara musu sosai, ba wanda ke daukar kayayyakin da aka watsi da su a kan hanya, suna da karfin zuciya sosai wajen yaki, a karshe dai sun hallaka dukan 'yan fashin nan.

A shekarar 1562, Qi Jiguang ya jagoranci sojojinsa don kai farmaki kan 'yan fashin teku na kasar Japan da ke tsugunewa a tsibirorin Fujiang na kasar Sin har shekaru da yawa, bayan da sojojin gidan Qi suka hallaka su, sai suka yada labarai cewa, sojoji sun gaji sosai, sun bukaci hutawa a cikin wani lokaci, wasu 'yan fashin teku na kasar Japan da ke boye a sauran wurare, da suka ji labarin nan, sai suka saki jikinsu, ba su tsaya kan bakanta su ba, amma ba zato ba tsammani sojojin gidan Qi suka kai farmaki gare su a dare, sun hallaka 'yan fashin nan kwata kwata, kai, har zuwa yau dai ana yada labarin nan a tsakanin jama'a.

Qi Jiguang ya yi yake-yake har cikin duk rayuwarsa, an kara masa mukamai da yawa, amma ya ce, wannan ne ba burinsa ba ne, fatansa shi ne babu yaki a tekun kasar mahaifa. Wannan ya bayyana niyyarsa ta kishin kasa sosai da sosai.(Halima)


1  2