Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 16:45:19    
Wani jarumin kasar Sin na zamanin da mai suna Qi Jiguang

cri

Qi Jiguang jarumin al'umma ne da kowa ya san shi a kasar Sin, shi ne ya jagoranci sojoji wajen yaki da 'yan fashi na kasar Japan da ke harar yankin kasar Sin a bakin teku tare da sakamako da yawa. An yada labarinsa a wurare masu yawa na kasar Sin.

A daular Ming na karni na 14 zuwa na 16, gungon 'yan fashi na kasar Japan suka kai hari a lardin Shandong da Zhejiang da Fujian da sauran wurare da ke bakin teku na gabashin kasar Sin, shi ya sa jama'a farar hula na kasar Sin sun sha barna sosai, kuma sun kira wadannan 'yan fashi da cewar 'yan fashin teku na Japan. A karshen karni na 16, harin da 'yan fashin teku na kasar Japan suke kaiwa sai kara tsananta suke yi, 'yan fashin teku sun kasance cikin wayo da kuzari sosai, kuma sun kashe mutane da yawa tare da kone abubuwa, ba su yi kome ba sai miyagun ayyuka, rundunar sojoji ta kasar Sin ba su da karfin maganinsu , shi ya sa jama'a farar hula suka kasance cikin mawuyacin hali sosai. A lokacin da 'yan fashin teku na kasar Japan suka yi barna sosai, sai aka tura Qi Jiguang a fagen yaki na maganin 'yan fashin teku a bakunan teku na kasar Sin.

An haifi Qi Jiguang a shekarar 1525 a garin Penglai na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, kakani kakaninsa dukansu su ne janarorin daular Ming. An bayyana cewa, tun lokacin da Qi Jiguang yake karami, sai shi kadai ne ya iya shirya yara wajen yin wasannin soja, ya ba da umurni bisa halin da ake ciki yadda ya kamata, kuma ya iya yin amfani da dabarun soja na jan baya ko ci gaba, sa'anan kuma ya mai da hankali sosai ga karanta littattafai iri iri da yawa, ya fahimci abubuwan da aka rubuta a cikin shahararrun littatafai da dabarun yaki na zamanin aru aru . A lokacin da ya cika shekaru 17 da haihuwa, sai ya ci gadon mahaifinsa ya zama wani mai ba da umurni ga sojoji na wurin da yake zama, a kai a kai ne ya kara matsayin mukaminsa, sarkin daular Ming ya kuma nada shi don ya zama wanda ke kula da harkokin yaki da 'yan fashin teku na kasar Japan.

1  2