Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 10:58:42    
Kasar Sin ta bukaci yin ayyuka da yawa wajen raya wasan tsalle-tsalle da guje-guje

cri

Game da yadda za a rage gibin da ke tsakanin 'yan wasan kasar Sin da na kasashen duniya da ke nuna fifiko a fannin wasan tsalle-tsalle da guje-guje wajen jikunan 'yan wasa, Mr. Feng ya yi bayanin cewa, nasarar da kasar Sin ta samu a gun wannan gasa ba za ta shaida cewa, kasar Sin za ta ci nasara kamar haka a gun taron wasannin Olympic na Beijing ba. Ya kara da cewa, kafin shekarar 2008, 'yan wasan kasar Sin sun nemi kyautata ingancin horo da kara samun fasahohin yin gasa. Ya ce,'a cikin gasar da aka yi a wannan gami, fiye da rabin 'yan wasan kasar Sin sun gwada gwanintarsu mafi kyau, sun karya matsayin bajinta nasu, wannan yana da muhimmanci sosai wajen makomarsu da bunkasuwarsu. Amma abin bakin ciki shi ne ya kasance da babban gibi a tsakanin gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta duniya da taron wasannin Olympic na Beijing. 'Yan wasanmu ba su da isassun kwarewa, suna bukatar kyautata kansu. A cikin shekaru 2 masu zuwa, wajibi ne 'yan wasanmu su karfafa kwarewarsu a lokacin horo don tabbatar da kara yin fintikau lami lafiya a cikin gasanni. A ganina, yin fintikau da kwarewar 'yan wasa dukansu suna da muhimmanci. Za mu dauki wasu matakai don ganin cewa, za a kara horar da 'yan wasa matasa ta hanyar sana'a. Za mu yi dabara za mu samar da sharudda, ta yadda za su sami damar yin takara da nagartattun 'yan wasan kasashen waje. Dole ne 'yan wasa su mallaki fasahohin yin gasannin duniya, wannan zai taimaka sosai gare su wajen shiga cikin taron wasannin Olympic da kuma gasar fid da gwani ta kasa da kasa.'(Tasallah)


1  2