Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 10:58:42    
Kasar Sin ta bukaci yin ayyuka da yawa wajen raya wasan tsalle-tsalle da guje-guje

cri

Ran 20 ga wata da dare, a nan Beijing, an rufe gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta kasa da kasa ta karo na 11, wadda aka yi kwanaki 6 ana yinsa. A cikin gasar da aka yi a wannan gami, saboda samun lambobin zinare 5, da azurfa 5 da kuma tagulla 7, kungiyar kasar Sin ta zama ta biyu a cikin dukan kungiyoyi masu shiga wannan gasa wajen samun lambobin zinare, ta kuma zama ta farko wajen samun lambobin yabo. Ko da yake ta ci nasara, amma ba ta yi girman kai ba, mutanen rukunin wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin sun nuna cewa, ko da yake an samu maki mai kyau a gun gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta kasa da kasa, amma wannan bai sa kaimi kan kasar Sin da ta sami babban ci gaba a cikin gasannin tsalle-tsalle da guje-guje a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 ba.

Babban malamin wasa na kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin kuma mataimakin darektan cibiyar kula da wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin Mr. Feng Shuyong ya bayyana cewa, saboda an soma horar da 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin ta hanyar sana'a a karkashin shugabancin malaman wasa tun daga lokacin yarantakarsu, shi ya sa suka nuna fifiko cikin dan lokaci kadan kawai. Ya ce, ''yan wasan kasar Sin matasa sun nuna gwanintarsu yadda ya kamata a gun wannan gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle ta matasa ta kasa da kasa, shi ya sa muna kan gaba a cikin dukan kungiyoyi masu shiga wannan gasa wajen samun lambobi. Wannan ya faranta rayukan mutane. Tun da can mun fi nuna karfi a gun gasar fid da gwani ta matasa, akwai dalilai da yawa da suka sa haka. 'Yan wasanmu sun fara samun horo ta hanyar sana'a tun daga yarantakarsu, an fi horar da su yadda ya kamata, in an kwatanta su da 'yan wasan kasashen waje, wadanda ba safai a kan horar da su yadda ya kamata ba.'

Mr. Feng yana ganin cewa, a cikin 'yan wasan kasar Sin matasa da suka jawo hankulan mutane saboda makin da suka samu a wannan gami, akwai wasu kadan daga cikinsu ne kawai za su dauki babban nauyi bisa wuyansu a cikin gasannin tsalle-tsalle da guje-guje a gun taron wasannin Olympic na Beijing, idan kasar Sin ta nemi samun lambobin yabo a gun wannan muhimmin taron wasanni, za ta dogara da wasu 'yan wasanta taurari, kamar shi Liu Xian, dan wasan gudun ketare shinge mai tsawon mita 110. Ya ce,'ina tsammani cewa, mai yiwuwa ne wasu kadan daga cikinsu ne kawai za su taka muhimmiyar rawar a zo a gani, wajibi ne mun fi dogara da 'yan wasanmu masu karfi da su yi ta daga karfinsu da kyautata kwarewarsu a fannonin yin gasa da nuna gwaninta da tsayayyiyar kwarewar samun maki mai kyau a cikin wasu muhimman gasanni da za a yi a cikin shekaru 2 masu zuwa, suna bukatar yin ayyuka da yawa, haka kuma mu mutanen rukunin wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin za mu yi iyakacin kokarinmu.'

1  2