Game da 'yan wasan motsa jiki, ban da samar musu tabbacin zaman lafiya, lafiyar jikinsu kuma ya zama wani muhimmin abu ne sosai. Mr. Guo Jiyong, shugaban sashen likitanci na kwamitin shirye shirye na wannan gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya ya bayyana cewa, kwamitin shirye-shirye ya tsara shiri sosai ga ayyukan yin ceto da warkar da cututtukan 'yan wasa bisa abubuwan da ake bukata domin wasannin Olimpic. Ya ce "Yanzu mun samu tabbaci sosai ga ayyukan likitanci na yin ceto da warkar da cututtukan 'yan wasa, mun kafa tashoshin duba marasa lafiya guda 3 cikin filin wasan, sa'an nan kuma mun da akwai wata cibiyar aikin likitanci".
Kowa ya sani cewa, matsalar "magani mai sa kuzari" wata babbar matsala ce ga wasannin motsa jiki, sabo da haka yanzu wani wasan Olimpic da aka yi tare da nasara ba zai rabu da aikin binciken kwayoyi masu sa kuzari cikin tsanaki ba. Mr. Zhao Jian, shugaban sashen duba magani mai sa kuzari na wannan gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya ya bayyana cewa, "Idan an kwatanta wannan gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya da na sauran irin wannan gasannin da aka yi a da, sai a ga cewa, an samu sikeli mafi girma a gun wannan gasa wajen binciken magani mai sa kuzari. Yawan mutane masu sa ido a gun wannan gasa suma suna da yawan gaske". 1 2
|