Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-18 18:14:32    
Birnin Beijing yana share fage domin wasannin Olimpic ta hanyar yin gasar guje guje da tsalle tsalle ta samarin duniya

cri

Gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya ta 11 wadda aka shafe kwanaki 6 ana yin ta yanzu a nan birnin Beijing. Sabo da wannan gasar da ake yi ta zo kusan sauran shekaru 2 kawai da bude wasannin Olimpic na shekarar 2008 na Beijing, kuma ta zama wata gasar da ake yi bisa matsayin koli na kasashen duniya, shi ya sa wanna gasa da ake yi ba kawai domin duba karfin dahir na 'yan wasa samari ga yin wasannin Olimpic na shekarar 2008 na Beijing ba, hatta ma ta samar wa birnin Beijing damar tattara fasahohin ayyukan shirye-shirye da kafa wata kungiyar kwararrun mutane domin yin wannan wasannin Olimpic. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani cikakken bayani game da wannan labari.

Gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya wata gasa ce da ake yi bisa matsayin koli na kasashen duniya wajen sassan wasannin guje guje da tsalle tsalle na kasa da kasa, gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya ta 11da ake yi daga ran 15 zuwa ran 20 ga wata a nan birnin Beijing ta zama wata gasa mafi girman sikeli cikin tarihin yin gasannin guje guje da tsalle tsalla na samarin duniya, 'yan wasan da suke halartar gasar sun zo ne daga kasashe da jihohi 180 na duniya kuma yawansu ya kai 1451.

Aikin kiyaye zaman lafiya ya zama aiki mafi muhimmanci ga yin wasannin motsa jiki. Mr. Cao Dongxiang, mataimakin shugaban sashen kiyaye zaman lafiya da zirga-zirga na wannan gasar guje guje da tsalle tsalle ta cin kofin samarin duniya ya bayyana cewa, "A lokacin da muke tafiyar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a gun wannan gasar, mun yi amfani da matakan da muka dauka bayan da muka yi bincike cikin wani lokacin da ya wuce domin kiyaye zaman lafiyar filaye da dakunan wasannin Olimpic".

1  2