Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 15:22:52    
Ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a sun sami bunkasuwa lami lafiya a kauyukan kasar Sin

cri

Madam Wen Wen, wata jami'ar babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin tana ganin cewa, yin wasannin motsa jiki na jama'a yana da muhimmanci sosai ga dukan jama'ar kasar, musamman ma ga manoma. Ta ce,'muhimmin makasudi na masu aikin wasannin motsa jiki shi ne karfafa ingancin jikunan dukan 'yan kabilar kasar Sin. Babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar ta dauki matakai a jere a shekarar bana, ta yi amfani da zarafin taron wasannin Olympic na shekarar 2008, ta raya wasannin motsa jiki tare da taron wasannin Olympic. Muhimmin aiki shi ne karfafa ra'ayoyin motsa jiki a cikin zukatan dukan jama'ar kasar, da ilmantar da su wajen samun dabarun yin motsa jiki ta hanyar kimiyya, da kafa kungiyoyin motsa jiki na fararen hula da gina filayen motsa jiki gare su, musamman ma ga manoma, a sa'i daya kuma, an yi wasannin motsa jiki na jama'a masu ban sha'awa iri daban daban, ta yadda mutane za su shiga cikin wasannin motsa jiki na jama'a, a karshe da za a karfafa ingancin jikunan dukan 'yan kabilar kasar Sin.'

Mr, Xing Chensheng, mai ba da shawara kan yawon shakatawa na hukumar gnndumar Youyu shi ma yana ganin cewa, raya wasannin motsa jiki na jama'a ya taimakawa raya tattalin arziki sosai. Musamman ma a kauyukan kasar, ainihin manufofin gina kauyuka wato 'neman samun wayewar kai da wadatuwa da bunkasuwa' ya yi daidai da na ra'ayin da wasannin Olympic ya yada wato 'Higher, Swifter, Stronger'. Ya kara da cewa,'ba zai iya mallakar kome ba, sai yana da lafiya. Ba za su iya raya tattalin arziki ba, sai lafiyar mutane yana da kyau a dukkan zukatansu da jikunansu. Ko ta halin kaka ta sa kaimi kan neman samun lambobin yabo a gun taron wasannin Olympic, da raya wasannin motsa jiki bisa manufar neman 'Higher, Swifter, Stronger', ya kamata wata kasa ta mayar da yin kira ga jama'arta da su yi motsa jiki a matsayin babban aikinta. A zarihi kuma ainihin manufofin neman 'Higher, Swifter, Stronger' da neman samun wayewar kai da wadatuwa da bunkasuwa duk daya ne. Makasudinsu duk daya ne.'

Bisa labarin da aka bayar, an ce, babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar ta mayar da gundumar Youyu a matsayin sansanin musamman na yawon shakatawa, ta kuma yi hadin gwiwa da ita wajen gina sansanoni 5. (Tasallah)


1  2