Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 15:22:52    
Ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a sun sami bunkasuwa lami lafiya a kauyukan kasar Sin

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, saboda mutanen kasar Sin sun kara mai da hankulansu kan lafiyarsu, shi ya sa suka shiga cikin wasannin motsa jiki ka'iu da na'iu. Ban da wannan kuma, yin wasannin motsa jiki na jama'a ya ba da babbar gudummowa wajen bunkasuwar tattalin arzikin wasu wuraren kauyukan kasar Sin. Lokacin da yake ziyarar gundumar Youyu na lardin Shanxi na arewa maso yammacin kasar a kwanan baya, wakilinmu ya gano cewa, wasannin motsa jiki na jama'a ya sami ci gaba sosai a kauyukan kasar Sin.

A shekarun baya da suka wuce, gundumar Youyu ta yi amfani da halin musamman na wasannin motsa jiki, ta karfafa ingancin aikin yawon shakatawa, ta rika shirya manyan tarurukan wasannin motsa jiki na kasar, ta yadda ta ingiza bunkasuwar aikin yawon shakatawa ta dukkan gundumar.

Mataimakin shugaban gundumar Mr. Lan Cheng ya bayyana wa wakilinmu cewa, halin musamman na wasannin motsa jiki na jama'a da gundumar Youyu take da shi shi ne, yin wasannin motsa jiki don jin dadin jama'a, da kuma ingiza bunkasuwar aikin yawon shakatawa. Ya ce,'gundumar Youyu ta ingiza bunkasuwar aikin yawon shakatawa ta hanyar wasannin motsa jiki a 'yan shekarun da suka gabata. Hukumar gundumar ta zuba jari, ta samar da manyan gine-ginen motsa jiki na jama'a, da gina filin shakatawa da filin motsa jiki, sa'an nan kuma, ta zuba jari wajen gina babban dakin wasanni a shekarar da muke ciki. Da farko, mun raya ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a, ta haka jama'a sun ji dadin zaman rayuwarsu. Na biyu kuma, mun ingiza bunkasuwar aikin yawon shakatawa ta hanyar wasannin motsa jiki, yanzu muna tsara wasu shirye-shiryen motsa jiki a waje, kamar su farauta da kuma gudun kankara daga babban dutse. '

1  2