Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-24 15:50:47    
Yin watsi da shan taba

cri

Game da wasu mutane da ke sha'awar shan taba sosai, ya kamata su sha magunguna yayin da suke yin watsi da shan taba. Wadannan magunguna za su rage damuwa da bakin ciki bayan da suka daina shan taba.

To, mun riga mun gaya muku muhimman abubuwa kan yin watsi da shan taba. Amma wani muhimmin abu daban shi ne, idan ka riga ka yi watsi da shan taba a cikin watanni shida, dole ne ka ci gaba da kiyaye halin nan da kake ciki domin gujewa daga sake komawa shan taba.

Madam Lu Xiuxia ta riga ta sha taba har shekaru 30. A shekara ta 2004, ta fara yin watsi da shan taba, amma bayan shakara guda, ta sake komawa shan taba, yanzu tana sha taba a kalla hudu a ko wace rana. Ta ce, "abokana sun tambaye ni, don me ki sake komawa shan taba? Kai, ban da shan taba, ba na yin wasu abubuwa masara kyau."

A hakika dai, sake shan taba ba abin tsoro ba ne, kada ka ji kunya da kuma shakkar jarumtakarka wajen yin watsi da shan taba. Sabo da bisa kidayar da aka yi, an ce, kamar wani mutum, bayan da ya yi watsi da shan taba har sau bakwai, sai ya iya cin nasara kwata-kwata.(Kande Gao)


1  2  3