Kamar yadda Madam Yang ta fada, akwai muhimman abubuwa uku wajen yin watsi da shan taba. To, da farko, bari mu yi managa kan niyya. Idan ana so a tsai da yin watsi da shan taba, to dole ne ya fahimci mumunar rawa da shan taba ya taka ga lafiyar jiki. Wata 'yar birnin Beijing mai suna Li Guizhen ta gaya mana cewa,
"shan taba bai ba da taimako ga lafiyar jiki ba, yanzu ni wata tsohuwa ce, idan na yi tari, majina da na tofa tana da launin baki."
Gwaje-gwajen kimiyya masu yawa da aka yi sun shaida cewa, shan taba yana da mumunar illa sosai ga lafiyar mutane. Kai ko saurayi ne ko tsoho ne, kana shan taba cikin dogo lokaci ko gajerren lokaci, kamata ya yi ka sani, yin watsi da shan taba ya fi ci gaba da shan taba kyau ga lafiyar jikinka. Watakila idan ka yi watsi da shan taba, ba za ka ji dadi sosai ba cikin gajerren lokaci, amma ya kamata ka sani, wannan ba zai haddasa cututtuka ba.
Ban da wannan kuma, wani muhallin da ya dace da yin watsi da shan taba yana da muhimmanci sosai.
Yanzu, kasashe fiye da 190 sun riga sun daddale yarjejeniyar kayyade shan taba, kuma ba a amince da yi tallar taba ba, ban da wannan kuma kasashe daban daban suna fitar da dokoki da ka'idoji masu yawa kan hana shan taba.
Bugu da kari kuma idan kana so ka yi watsi da shan taba, don Allah ka gaya wa iyalanka da makwabtanka da kuma abokanka domin su taimake ka. A waje daya kuma ka iya neman wani aboki domin ku yi watsi da shan taba tare, idan ku nuna goyon baya ga juna, to yin watsi da shan taba zai fi sauki gare ku.
1 2 3
|