Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-21 19:30:10    
Ana dudduba ' Doka kan cin gashin kai tsakanin shiyyoyin kananan kabilu' bisa babban mataki a kasar Sin

cri

Bunkasa sha'anin ilmantar da ' yan kananan kabilu, wani muhimmin batu ne dake cikin wannan doka,wadda kuma ta tanadi cewa dole ne gwamnatocin matakai daban daban na kasar Sin su tallafa wa ' yan kananan kabilu ta hanyoyi daban daban. Mr. Xu Jialu, mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya fadi, cewa : ' Har kullum ya kasance da gibi tsakanin kananan kabilu da kabilar Han a fannin ilmantarwa da matsayin zurfin ilmi. Don haka, ya kamata a kara kyautata aikin ba da ilmi ga 'yan kananan kabilu'.

Ban da maganar shiga makaranta da kananan yara ke yi, 'yan kabilar Maonan sun kuma bayana sauran wahalhalun da suke sha a cikin zaman rayuwarsu. Dan kabilar mai suna Shi Peichun ya fadi, cewa : ' Iyalina na da mutane biyar. Lallai mun sha wahala wajen ganin likita. Manoma sukan biyan wassu kudade wajen samun magungunan sha saboda har yanzu ba mu samu tabbaci a fannin likitanci daga al'ummar kasa ba'.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu akwai kananan kabilu 44 na kasar Sin da suka kafa hukumomi masu cin gashin kai ; kuma kashi 71 cikin kashi 100 bisa jimlar 'yan kananan kabilu na duk kasar suna more ikon kai a shiyyoyin da suke zaune ; Kazalika, fadin shiyyoyin kananan kabilu da ake aiwatar da manufar cin gashin kai ya dauki kimanin kashi 64 cikin 100 bisa fadin duk kasa baki daya.

Nan da watanni biyu masu zuwa, za a gudanar da aikin duddubawa a jihar Xinjiang, da jihar Tibet da kuma lardin Guangxi da dai sauran shiyyoyi na matakin lardi, ta yadda za a kawar da tulin wahalhalun da ' yan kanana kabilu suke sha tun da wuri. ( Sani Wang )


1  2