Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-21 19:30:10    
Ana dudduba ' Doka kan cin gashin kai tsakanin shiyyoyin kananan kabilu' bisa babban mataki a kasar Sin

cri

Hukumar iko ta koli ta kasar Sin wato kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin yana nan yana dudduba ' Doka kan cin gashin kai tsakanin shiyyoyin kananan kabilu' bisa babban mataki, wadda ake aiwatar da ita har na tsawon shekaru 22. Ma'aikatan kwamitin din-din-din na majalisar suna yin wannan aikin duddubawa ne a shiyyoyi 20 na matakin lardi, inda za su sanya matukar karfi wajen kawar da wahalhalun da 'yan kananan kabilu suke sha sakamakon muhimman matsalolinn dake kasancewa cikin yunkurin aiwatar da wannan doka. Ko shakka babu 'yan kananan kabilu 55 za su ci gajiyar wannan doka.

Jama'a, kuna sane da, cewa kasar Sin wata babbar kasa ce mai yawan kabilu. A cikin kabilu 56 da take da su, ban da kabilar Han, sauran kabilu 55 da ba su da mutane da yawa, ana kiransu ' Kananan Kabilu', wadanda yawan mutanensu ya zarce miliyan dari daya.

Domin kara kiyaye iko da moriya na kanana kabilu da kyau da kuma daidaita maganganun dake gabansu kamar yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin ta mayar da cin gashin kai tsakanin shiyyoyin kananan kabilu a matsayin wani muhimmin tsarin siyasa na kasa, wanda ya tanadi, cewa a iya kafa hukumar cin gashin kai da tafiyar da ikon kai a wuraren da 'yan kananan kabilu ke zaune a cunkushe. ' Doka kan cin gashin kai tsakanin shiyyoyin kananan kabilu' da aka soma aiwatar da ita a shekarar 1984, wata muhimmiyar doka ce da ake bi wajen shimfida tsarin kai gashin kai a shiyyoyin kananan kabilu, wadda take shafar fannin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da kuma na zamantakewar al'umma da dai sauran fannoni.

Yanzu, 'yan kananan kabilu masu yawan gaske suna zaune a shiyyoyi kan tsaunuka dake can nesa ba kusa ba saboda dalilin tarihi da na halittu. Kabilar Maonan tana daya daga cikinsu. Yawan 'yan kabilar ya kai 100,000 kawai, wadanda suke zama a kauyuka kan wani babban tsauni a lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Ma'aikatan kungiyar duddubawa sun gano wahalhalun da 'yan kabilar suke sha. Madam Shi Rei , 'yar kabilar Maonan kuma jami'in kauyen kabilar ta furta, cewa ' Yanzu kusan dukan kananan yara suna iya shiga makaranta domin kasarmu tana aiwatar da manufar ba da ilimi ga kowa. Amma yaran dake zaune a shiyyoyi kan tsaunuka masu nisa suna shan wahala saboda sukan bata awa biyu ko uku kan hanyar zuwa makaranta'.


1  2