Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-20 17:04:40    
Kasar Sin tana gudanar da ayyukan share fage a kan binciken duniyar wata yadda ya kamata

cri

Idan kasar Sin ta iya harba wannan tauraron dan adam mai lambar "Chang'e" 1 wanda zai yi shawagi a kewayen wata don binciken duniyar wata daidai ranar da aka tsayar, to, za a iya kyautata zato cewa, a karo na farko, tauraron dan adam da kasar Sin ta harba zai yi shawagi a sararin samaniya da ke da nisan kilomita dubu 400 daga duniyarmu, kasar Sin kuma za ta fara binciken duniyar wata daga tauraron dan adam.

Malam Sun Laiyan ya kara da cewa, ganin cewa aikin binciken duniyar wata wani babban aikin binciken sararin sama ne mai sarkakiya sosai, mai yiwuwa ne, kasar Sin za ta hada guiwarta da kasashen waje don gudanar da wannan aiki. Ya ce, "yanzu, mun riga mun kammala aikin tsara fasalin tauraron dan adam mai lambar "Chang'e "1, sabo da haka ba za mu hada guiwarmu da kasashen waje a fannoni da yawa ba, yayin da muke sarrafa wannan tauraron dan adam. Amma za mu kara neman kasashne da za mu iya hadin guiwa a tsakaninmu don ci gaba da aiwatar da shirinmu. "

Malam Sun Laiyan ya ci gaba da cewa, ban da wannan kuma kasar Sin ta yi shirin binciken duniyar rana ta hanyar tauraron dan adam, kuma yana fatan za a hada guiwa a tsakanin Sin da kasashen waje a wannan fanni.

Madam C. Hartman, jami'ar hukumar NASA ta kasar Amurka ta bayyana cewa, "shugaban hukumar NASA ta kasar Amurka zai kawo ziyara a kasar Sin a watan Satumba mai zuwa, a nan ne bangarorin Amurka da Sin za su yi tattaunawa a kan hadin guiwar da za su yi a tsakaninsu." (Halilu)


1  2