Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-20 17:04:40    
Kasar Sin tana gudanar da ayyukan share fage a kan binciken duniyar wata yadda ya kamata

cri

A gun taron duniya kan binciken kimiyyar sararin samaniya da ake yi yanzu a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, wani jami'in kasar ya bayyana cewa, kasar Sin tana gudanar da ayyukan share fage a kan binciken duniyar wata yadda ya kamata, ya kuma kyautata zaton cewa, a shekarar badi, kasar Sin za ta harba tauraron dan adam na farko da zai yi shawagi a kewayen wata, don binciken duniyar wata daidai ranar da aka tsayar.

Bayan da kasar Sin ta yi nasarar harba kumbuna masu daukar 'yan sama-jannati guda biyu a shekarar 2003 da ta 2005, a galibi dai, bangaren 'yan kimiyya masu binciken sararin samaniya na duniya suna ganin cewa, yanzu kasar Sin ta riga ta kware wajen harba tauraron dan adam don binciken duniyar wata. Yau da shekara biyu da suka wuce, kasar Sin ta yi shelar fara aiwatar da shirinta mai suna " Chang'e" na binciken duniyar wata, kuma za ta yi kokarin harba tauraron dan adam na farko don binciken duniyar wata a shekarar badi. Malam Sun Laiyan, shugaban hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin ya bayyana a gun taron kasa da kasa kan binciken kimiyyar sararin samaniya cewa, kasar Sin za ta harba wannan tauraron dan adam ne don binciken duniyar wata a shekarar badi. Ya ce, "a galibi dai, kasar Sin za ta harba tauraron dan adam da zai yi shawagi a kewayen wata ne don binciken duniyar wata a shekarar badi. Amma ko shakka babu, a kan gamu da wahalhalu, yayin da ake gudanar da ayyukan fitar da wani irin watan dan adam na sabon salo. Idan mun iya kawar da duk wahalhalun, to, za mu iya harba wannan tauraron dan adam bisa shirin da muka yi."


1  2