A cikin dogon lokacin tarihi , an yi sinima mai sunan 'yan jam'iyyar kwaminisanci mata guda 8 , daga bisani an yi masa gyare-gyare da ya zama Wasan kwaikwayon Kun , daga baya ya taba samun sunan babbar muryar Kunshan. A lokacin da sabo da aka yi wasan a kan dakalin da ake shirya a gindin Tudu , shi ya sa a kan kira shi cewa , wasan operar tudun Kunshan . Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin an fara yin amfani da Wasan kwaikwayon Kunshan . Wannan wasan yana yaduwa a kudancin lardin Jiangsu da birnin Shanghai . Wannan wasan daya ne daga cikin wasannin kwakwayo mafiya kasance da tasiri mai kyau ga matasa .
Ban da birnin Beijing , a wurare daban daban an yi bikin shagulgula don tunawa da kafuwar jam'iyyar kwaminsanci ta kasar Sin . A ma'adinin kwal na Shendong na Jihar Mongolia ta gida dake arewaxin kasar Sin , ma'aikata sun yi gasar wake-wake , inda suka bayyana kaunarsu ga jam'iyyar . Kang Shengle , wani mahakin kwal ya gaya wa wakilion Rediyon kasar Sin cewa , kafin shekarar 1949 , iyalinsa matalauta ne kwarai da gaske . Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar Sin , a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminisanci , zaman rayuwar iyalinsa ya kyautatu sosai . Yanzu iyalinsa suna jin dadi ainu.
To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri . (Ado) 1 2
|