Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 20:59:47    
Kungiyar hadin kai ta Shanghai

cri

Tun daga shekara ta 2004 kuma, kungiyar hadin kai ta Shanghai ta fara aiki da tsarin masu sa ido. A watan Yuni na wannan shekarar, an yi taron koli na karo na hudu na kungiyar a birnin Tashkent, inda kasar Mongoliya ta sami matsayin mai sa ido. A gun taron koli na kungiyar da aka yi a karo na 5 a birnin Astana a watan Yuli na shekara ta 2005 kuma, an kuma yanke shawarar bai wa kasashen Pakistan da Iran da Indiya matsayi na masu sa ido.

Tun lokacin da aka kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai, sai bi da bi ne kasashen kungiyar suka fara aiwatar da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tsaro da tattalin arziki da al'adu da aikin soja da doka da dai sauransu, an kuma yi ta karfafa hadin gwiwa. Tun bayan aukuwar al'amarin ranar 11 ga watan Satumba, kasashen kungiyar suka inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin yaki da ta'addanci, musamman ma yaki da rukunoni uku na 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi da kuma masu neman ballewa na shiyyar. A fannin tattalin arziki ma, an kulla 'tsarin ka'idojin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin bangarori da dama na kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai' da kuma matakan da za a dauka don tabbatar da tsarin ka'idojin kungiyar, bayan haka, an kuma kafa kungiyoyin musamman bakwai da suka hada da kungiyar binciken ingancin kayayyaki da ta kula da kwastan da cinikin zamani da bunkasa zuba jari da sufuri da makamashi da kuma sadarwa, don su kula da daidaita hadin gwiwar a wadannan fannoni.

Yawan fadin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai ya zarce murabba'in kilomita miliyan 30 baki daya, kuma yawan mutanensu ya kai biliyan 1 da miliyan 489. A kan kira taron shugabannin kasashen kungiyar a shekara shekara. (Lubabatu Lei)


1  2