Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 20:59:47    
Kungiyar hadin kai ta Shanghai

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun alhaji.Aliyu Musa, mazauni Jalingo, jihar Taraba ta tarayyar Nijeriya. A cikin E-mail da ya aiko mana ya ce, daga shafinku na internet ne na ga an ce, an yi taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai. To, amma shin kungiyar hadin kai ta Shanghai wace irin kungiya ce?

To, bari mu yi muku bayani a kan wannan kungiya, wato kungiyar hadin kai ta Shanghai.

Ita kungiyar hadin kai ta Shanghai, da ma asalinta shi ne 'tsarin ganawa na Shanghai da ke tsakanin kasashe biyar', wato Sin da Rasha da Kazakhstan da Kyrghyzstan da kuma Tadzhikistan. A ranar 14 ga watan Yuni na shekara ta 2001, shugabannin kasashen nan biyar sun yi ganawa a karo na shida a birnin Shanghai, inda kasar Uzbekistan ita ma ta shiga shawarwarin a matsayin daidai da na sauran kasashe biyar. Kashegari kuma, wato ranar 15, shugabannin kasashen shida sun yi ganawa a karo na farko a tsakaninsu, kuma sun daddale 'sanarwar kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai', don sanar da kafuwar kungiyar.

A watan Nuwamba na shekara ta 2001, firaministocin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai sun yi ganawa a karo na farko a tsakaninsu a birnin Alma-Ata na kasar Kazakhstan, inda suka sanar da kafa tsarin ganawa a tsakanin firaministocin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai a karkashin tsarin kungiyar. Daga baya, a watan Yuni na shekara ta 2002, an yi taron koli na karo na biyu na kungiyar hadin kai ta Shanghai a birnin St.Petersburg, inda shugabannin kasashen shida suka rattaba hannu a kan 'tsarin ka'idojin kungiyar hadin kai ta Shanghai'. Tsarin ka'idojin dai ya yi bayani sosai a kan manufar kungiyar hadin kai ta Shanghai da ka'idojinta da tsarinta da yadda ake gudanar da ita da dai sauransu, kuma daddale wannan tsarin ka'idoji da aka yi ya nuna cewa, kungiyar ta kafu bisa dokar duniya. A watan Mayu na shekara ta 2003 kuma, a karo na uku ne aka yi taron koli na kasashen kungiyar a birnin Moscow, inda aka daddale 'sanarwar shugabannin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai', kuma aka nada jakadan kasar Sin a Rasha a lokacin, wato Mr. Zhang Deguang a matsayin babban sakatare na farko na kungiyar. Daga bisani, a watan Janairu na shekara ta 2004, an kafa ofishin sakataren kungiyar hadin kai ta Shanghai a hukunce a nan birnin Beijing.

1  2