Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 15:54:37    
Wani mutum na zamanin da na kasar Sin mai suna Wang Anshi

cri

Wang Anshi ya yi matukar kokari wajen yin kwaskwarima, daga tattalin arziki zuwa harkokin kudi, har ma zuwa aikin kara jan damara, ya tsara sabbin dokoki a kansu. Wannan ne sauyawar dokokin shari'a da Wang Anshi ya yi, ya yi suna sosai a tarihin kasar Sin. Abubuwan da ke cikin sabbin dokokin sun bayyana hangen nesa da Wang Anshi ya yi bisa matsayinsa na dan siyasa. Bayan da aka aiwatar da sabbin dokokin nan cikin shekaru 5 da suka wuce, bisa dalilai da yawa , ciki har da sauyawar ra'ayin da sarki ya yi tare da bala'in halitta da kiyewar da manyan masu fada a ji suka yi har da tunanin camfe-camfen da aka yi a zamantakewar al'umma, sai aka tsayar da sauyin dokokin shari'a da Wang Anshi ya yi.

Wang Anshi shi ma wani mawallafi ne da ya yi suna sosai a tarihin kasar Sin. A duk zaman rayuwarsa, ya yi rubuce rubuce da yawa, littattafan da ya rubuta suna kunshe da fannoni da yawa, da akwai wakoki da siyasa da bayanan yawon shakatawa da dai sauransu.

Bayanan da ya rubuta sun ba da tasiri sosai ga bunkasuwar adabin kasar Sin a zamaninsa da kuma a zamanin yau.

Wang Anshi ya mutu a shekarar 1086 a lokacin da ya cika shekaru 66 bisa sanadiyar kamuwa da ciwo.(Halima)


1  2